Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Yi Ganawar Sirri da Wike Kan Zaben 2027, Rahoto

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Yi Ganawar Sirri da Wike Kan Zaben 2027, Rahoto

  • Za a yi babban zaben Najeriya na gaba a shekarar 2027 ne kuma tuni yan siyasa a kasar suka fara shiri kan zaben
  • Babbar jam'iyyar adawa ta PDP, za ta so kwace mulki daga hannun APC, don haka mambobinta ke kokarin ganin sun saita dandamalinsu
  • Kamar yadda sabon rahoto ya nuna, manyan jiga-jigan PDP biyu sun yi ganawar sirri a kwanan nan, inda suka tattauna batutuwan kafin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Wani rahoto da ke zuwa ya bayyana cewa Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya kana da Nyesom Wike a kwanan nan.

Legit Hausa ta rahoto cewa Wike shine minista babban birnin tarayya kuma shugaban kungiyar G5.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Kungiyar G5 ita ce ta fusatattun gwamnonin PDP da suka ki marawa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP baya, saboda suna ganin ya kamata ace an mika mulki daga arewa zuwa kudu.

Bala Mohammed ya gana da Nyesom Wike
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Yi Ganawar Sirri da Wike Kan Zaben 2027, Rahoto Hoto: @SenBalaMohammed, @GovWike
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: “Bala na hararar kujerar shugaban kasa", majiya

An tattaro cewa kungiyar gwamnonin PDP na shirin daidaita babbar jam'iyyar adawa gabannin 2027.

Ganawar da ake zargin ya gudana tsakanin Gwamna Mohammed da Wike an yi shi ne a cikin sirri, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.

Jaridar ta ce rade-radin ganawarsu ne yasa Wike ya ayyana cewa ba shi da kudirin son zama shugaban kasa a 2027.

Jaridar ta nakalto majiyar na cewa:

"Bala yana da sha'awa kan kujerar shugaban kasa a 2027 kuma tuni ya fara dike a PDP da fadin jam'iyyar."

Kara karanta wannan

“Idan ba’a kira ni dan midiya ba ɗan uwarki za’a kira ni” Na hannun daman Ganduje ya wanke budurwa

Majiyar ta kara da cewar:

"Kungiyar gwamnonin PDP na sha'awar sauya fasalin jam'iyyar amma wasu muhimman kararrakin zabe sun janye hankulan wasu mambobinta."

Atiku da Mohammed suna fafatawar neman iko

A wani labarin, mun ji cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zabukan 2019 da 2023, yana kulla-kulla don ganin ya ci gaba da rike jam'iyyar.

Sai dai kuma, hankalinsa da na masu yi masa biyayya bai kwanta da mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Illiya Damagum ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng