Kotu Ta Kama Tsohon Minista, Saleh Mamman da Aikata Laifuffuka 12 a Mulkin Buhari

Kotu Ta Kama Tsohon Minista, Saleh Mamman da Aikata Laifuffuka 12 a Mulkin Buhari

  • Kotu ta gamsu da hujjojin hukumar EFCC a shari'ar da ake zargin tsohon ministan lantarki, Saleh Mamman da karkatar da Naira biliyan 33.8
  • Kudin da ake zargin Mamman da wawurewa sun kunshi wadanda gwamnatin marigayi Buhari ta fitar domin aikin gina tashar Mambila
  • Rashin halartar tsohon ministan ya sa babbar kotun mai zama a Abuja ta dage karanto hukuncin da ta yanke masa zuwa wani lokaci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta samu tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, da aikata laifuffuka 12 da suka shafi zamba da safarar kudade.

A hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho ya yanke ranar Alhamis, kotun ta ce hukumar EFCC ta gabatar da hujjoji masu karfi da suka tabbatar da laifin tsohon ministan ba tare da wata shakka ba.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya samu sassauci da kotu ta ba shi damar jinya a hannun ICPC

Saleh Mamman.
Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman Hoto: Nafiu Bashir Yahaya
Source: Facebook

Kotu ta gamsu Mamman ya sace 33.8bn

Vanguard ta ce Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da ke cikin karar da hukumar yaki da rashawa ta EFCC mai lamba FHC/ABJ/CR/273/2024 ta shigar a kansa.

An tabbatar da cewa Mamman, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, na da hannu wajen karkatar da kudaden gwamnati da suka kai kusan Naira biliyan 33.8 ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta kuma gano cewa ya biya Dala 655,700, kwatankwacin Naira miliyan 200, domin sayen wani gida a Abuja ba tare da amfani da cibiyar hada-hadar kudi ba.

Ina kudin tashar Mambilla suka yi?

Haka kuma, an same shi da laifin cin amana kan kudaden da gwamnatin tarayya ta fitar domin ayyukan tashoshin samar da wutar lantarki na Mambilla da Zungeru.

Mai shari’a ya bayyana cewa mafi yawan kudaden an karkatar da su ne ta hannun 'yan canji (BDC), wadanda suka mayar da kudaden zuwa kudin kasashen waje kafin mika wa wanda ake kara.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

“Shaidun da masu gabatar da kara suka kawo sun fi karfin karamar kariyar da wanda ake kara ya gabatar,” in ji Mai Shari’a Omotosho.
Hedkwatar hukumar EFCC.
Hedkwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abuja da jami'anta a bakin aiki Hoto: EFCC Nigeria
Source: Twitter

Alkali ya caccaki tsohon ministan

Mai shari’ar ya nuna takaicinsa cewa tsohon ministan bai yi kokarin barin tarihi mai kyau a bangaren wutar lantarki ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

“Maimakon ya samar da wani abin tarihi wajen magance matsalar rashin wutar lantarki a kasar nan, wanda ake kara ya koma yana more rayuwa a kan dukiyar talakawa."
“Ba abin mamaki ba ne yadda har yanzu ‘yan Najeriya ke cikin duhu,” in ji shi.

Mamman bai halarci zaman kotu ba

Sai dai wanda ake kara bai halarci zaman ba lamarin da ya sa kotun ta dage yanke masa hukuncin da za a zartar, yayin da EFCC ta nemi a bayar da sammacin kama shi.

Lauyan wanda ake kara, Mohammed Ahmed, ya shaida wa kotun cewa tun bayan sanar da ranar yanke hukunci a ranar Talata, ba a san inda Mamman yake ba.

Kotu ta amince a karbe kadarorin Sylva

Kara karanta wannan

An gabatar bidiyo a kotu, mutum 2 suna da masaniyar shirin yi wa Tinubu juyin mulki

A wani rahoron, kun ji cewa kotu ta ba hukumar EFCC umarnin ƙwace wasu manyan kadarori guda tara da ke da alaƙa da tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva.

Mai shari'a Obiora Egwuatu ne ya bayar da wannan umarnin ne bayan lauyan hukumar EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya shigar da buƙatar hakan a gaban kotu.

Kadarorin suna yankuna masu daraja a cikin birnin Abuja, waɗanda suka haɗa da manyan gine-gine da rukunin gidaje na alfarma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262