Masu Garkuwa Da Mutane
Wasu yan ta'adda sun far ma al'umman wasu kauyuka uku a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, sun halaka mutane takwas tare da jikkata wasu uku a harin.
Al'umman garin Pegi da ke babbar birnin tarayya Abuja, sun gudanar da zanga-zangar lumana a safiyar yau Litinin, sun yi wa ofishin ministan birnin tarayya zobe.
Wasu yan bindiga sun kai farmaki yankin Gundum Hausawa da ke garin Bauchi a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, sun halaka mutane biyu mace da namiji a harin.
Wasu masu garkuwda mutane sun sace mutane da yawa a wani hari da suka kai yankin Kuje, da ke babbar birnin tarayya, Abuja a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba.
Yan bindiga da ba a san ko su waye ba a daren ranar Talata, sun sace tsohon kwamishinan ilimi na jihar Nasarawa, Cif Clement Uhembe a gidansa da ke garin Lafia.
Wasu mahara sun kai wa mamba mai wakiltan mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Rt.Hon. Nicholas Garba Sarkin Noma, da wasu mutane da ke cikin motarsa hari.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce wani shugaban yan bindiga ya taba rokonsa a yayin wata ganawa, cewa a daina yadawa idan jami’an tsaro suka kama su.
Wasu yan bindiga sun kashe mutum biyar, ciki harda wani basarake a garin Wereng da ke karamar hukumar Riyom a jihar Filato, a yau Talata, 6 ga watan Oktoba.
Dakarun rundunar sojoji sun ragargaji yan bindiga a hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun yi nasarar kawar yan ta'addan biyu da jikkata wasu, sun kwato bindigogi biyu.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari