Tashin Hankali: An Gano Gawar Mutum da Aka Fille wa Kai a Harabar Jami’ar Jos

Tashin Hankali: An Gano Gawar Mutum da Aka Fille wa Kai a Harabar Jami’ar Jos

  • An gano gawar wani mutum mai matsakaicin shekaru babu kai a wata gonar da ke cikin harabar Jami’ar Jos, jihar Filato
  • Lamarin ya jawo fargaba tsakanin ɗalibai da ma’aikatan jami’ar yayin da ake ci gaba da bincike kan mutumin da yadda aka kashe shi
  • Domin kawar da duk wata jita-jita, jami’an jami’ar sun ce wanda aka kashe manomi ne da ke zuwa gonar akai-akai, ba ɗalibi ko ma’aikaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Filato - An shiga rudani a cikin al’ummar Jami’ar Jos (UNIJOS) a ranar Talata bayan gano gawar wani mutum mai matsakaicin shekaru da aka fille wa kai a wata gona da ke cikin harabar jami’ar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a tabbatar da sunan mamacin a hukumance ba, sai dai an gano gawarsa ba tare da kansa ba, lamarin da ya jawo fargaba tsakanin ɗalibai, ma’aikata da mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya cika alkwari, ya bude kasuwar zamani da ta lakume Naira biliyan 2.98

An tsinci gawar wani mutum da aka fille masa kai a jami'ar Jos
Babbar kofar shiga jami'ar Jos da ke jihar Filato. Hoto: UGC
Source: Twitter

An tsinci gawa a jami'ar Jos

Wani ɗalibin jami’ar, dan aji uku, Pius Atok, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa an gano gawar ne a wata gona da ke cikin yankin jami’ar.

“An gano gawar ne da safiyar yau a wata gona da ke kusa da harabar jami’ar. Abin da muka fahimta shi ne wanda aka kashe ba ɗalibi ba ne kuma ba ma’aikacin jami’ar ba ne,” in ji shi.

Wani babban jami’in jami’ar da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana da manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa mamacin manomi ne da ya saba zuwa gonar domin noma.

“Wanda aka kashe ba ɗalibi ba ne kuma ba ma’aikaci ba ne. Mutane a yankin sun san shi saboda yakan zo gonar nan yana noma. Muna ganin ya zo da sassafe kamar yadda ya saba,” in ji jami’in.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a gano cikakken abin da ya faru ba, amma yanayin harin ya nuna cewa an kai masa hari ne da gangan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Guguwa mai karfi ta hallaka mutane, ta yi mummunar barna a Yobe

Ana ci gaba da bincike

Jami’in ya ce har yanzu ba a san waɗanda suka aikata kisan ba, amma ya nuna cewa yadda aka kai harin ya nuna cewa waɗanda suka aikata laifin sun zo ne da manufar kashe shi tare da ɗaukar kansa.

Ya ƙara da cewa an tuntubi iyalan mamacin, yayin da aka ɗauke gawar daga wurin da aka same ta.

Ya kuma bayyana cewa an sanar da shugabancin jami’ar game da lamarin, kuma sashen yaɗa labarai na jami’ar zai fitar da sanarwa a hukumance.

Sai dai, ba a samu nasara ba yayin da aka yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, SP Alfred Alabo.

An fille kan wata mata a Abuja

A wani labari, mun ruwaito cewa, mazauna Abuja sun gano gawar wata mata mai matsakaicin shekaru ba tare da kai ba a wani gini da ba a kammala ba.

Rahotanni sun nuna cewa warin da ke fita daga ginin, wanda ke yankin Bwari ne ya sa mutane suka shiga ciki suka gano gawar matar da aka fille wa kai.

Rundunar ‘yan sanda ta kwashe gawar zuwa asibiti tare da fara bincike domin gano ko wacece da yadda aka kashe ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com