Abinda ya sa na ke rokon 'yan sanda su kasheni: Bidiyon dan fashi

Abinda ya sa na ke rokon 'yan sanda su kasheni: Bidiyon dan fashi

Wani matashi da ya fada komar rundunar jami'an 'yan sanda saboda aikata fyade da fashi makami da fyade ya roki a kashe shi kawai gaba daya saboda hakan ne mafi alheri.

Da yake magana da manema labarai a hedikwatar rundunar tsaro, mai laifin, Adeniyi Ajayi, ya roki a kashe shi.

"Jama'a su kan firgita duk lokacin da na shiga gidansu, ni kuma sai na umarcesu su bani duk abinda nakeso a wurinsu saboda sun tsorata," a cewar mai laifin.

Da ya ke amsa tambayar manema labarai a kan zargin cewa ya aikata fyade ga mata fiye da 30, sai mai laifin ya ce; "ba gaskiya bane, na aikata hakan ne kawai sau uku; zan iya tuna wata matar aure da wata 'yar aiki. Wannan shine gaskiyar zance, ni bana karya."

"Na san ina aikata munanan aiyuka, saboda na fara fashi tun farkon shekarar 2019.

"Ni na fi so kawai 'yan sanda su kasheni saboda akwai dalilin da ya sa nake aikata laifi," a cewar Ajayi.

Da aka tamabayeshi ko menene dalilinsa, sai Ajayi ya ce; "ni dai ina da dalili, an kaini kurkuku a shekarar 2018, Kuma a can ne hadu da wadanda suka koyamin fashi.

"Babu wani mai taimakona a duniya, idan ba kasheni aka yi ba dole na cigaba da aikata laifuka.

"An fara kaini kurkuku ne saboda laifin sata, a can ne na hadu da 'yan fashin da suka bukaci na daina sata, mu hada kai muke yin fashi tare idan mun fita.

"Idan an sake mayar dani kurkuku zan hadu da wasu manyan 'yan fashin da zan kara samun gogewa a hannunsu.

"Zan addabi Najeriya da aikata miyagun laifuka matukar aka barni na cigaba da rayuwa," kamar yadda Ajayi ya bayyana.

Kalli faifan bidiyonsa da jaridar Punch ta wallafa a rumbunta na faifan bidiyo:

A wani labarin daban, Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa an gurfanar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Filato, Yakubu Chocho, a gaban wata babbar kotu da ke yankin Kasuwar Nama a Jos bisa tuhumarsa da aikata rashin gaskiya, tuggu da sata.

Tsohon shugaban ya gurfana a gaban kotun ne tare da sauran wasu mutane uku da ake tuhumarsu tare da shi.

DUBA WANNAN: Kano: Ministan Buhari ya kaddamar da wani katafaren gini da aka kammala a BUK

Sauran ragowar mutanen sune kamar haka; mai share-share; Helen Yakubu, maigadi; Samka Gyol, da wani kafinta; Adamu Garba.

Tsohon shugaban jam'iyyar da sauran mutane ukun sun musanta tuhumar da rundunar 'yan sanda ke mu su a gaban kotu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Helen da Samka su na aiki ne a hedikwatar jam'iyyar PDP da ke kan titin Yakubu Gowon a garin Jos lokacin da aka sace na'ura mai kwkwalwa mallakar daya daga cikin shugabannin jam'iyyar a jihar.

Bayan na'urar, an sace wasu kayayyakin mallakar Ishaku Chuntai, darektan gudanarwa na jam'iyyar PDP a jihar Filato. Kayan sun hada da wani alkalami na zinare da kayan shayi da jimillar kudinsu ta kai N135,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel