Ta'addanci: Mamba a majalissar dokokin jihar Benuwe ya samu matsuguni a kurkuku

Ta'addanci: Mamba a majalissar dokokin jihar Benuwe ya samu matsuguni a kurkuku

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Makurdi, babban birnin jihar Benuwe, ta bayar da umarnin a tsare Honarabul Jonathan Agbidye a gidan yari bisa zarginsa da hada baki domin aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane.

Kotun, a karkashin mai shari'a Mista Isaac Ajim, ta zartar da wannan hukunci ne a yau, Juma'a, yayin da aka gurfanar da Honarabul Agbidye, mamba mai wakiltar mazabar Kastina-Ala, a majalisar dokokin jihar Benuwe.

An yankewa Honarabuk Agbidye, mamba a jam'iyyar APC, wannan hukunci tare da wani mutum, Denen Zuamo, wanda ake zargi sun hada baki tare wajen aikata laifin.

Tun a ranar 22 ga watan Mayu dan sanda mai gabatar da kara, Fidelis Ogbobe, ya sanar da kotun cewa wasu 'yan fashi dauke da muggan makamai sun kwace wata mota kirar Toyota Hilux mallakar wata kungiya mai aiyukan jin kai.

An kwace motar ne a kan hanyar Katsina-Ala zuwa Tordonga a yankin karamar hukumar Katsina-Ala tare da tafiya da motar zuwa wani wuri da babu wanda ya sani.

Dan sandan ya sanar da kotun cewa an gano motar a wurin Honarabul Agbidye da Zuamo a Makurdi duk da sun sauya mata lamba.

A cewar Dan sandan, binciken rundunar 'yan sanda ya gano cewa Honarabul Agbidye da Zuamo da sauran wasu abokansu da yanzu ake nema sun kasance yara a wurin kasurgumin dan ta'adda; Terwase Akwaza.

Ta'addanci: Mamba a majalissar dokokin jihar Benuwe ya samu matsuguni a kurkuku
Majalissar dokokin jihar Benuwe
Asali: Depositphotos

Akwaza, wanda aka fi sani da suna 'Ghana', ya kasance hatsabibin dan ta'adda da har yanzu jami'an tsaro su ka gaza kamawa duk da irin yadda suke nemansa ruwa a jallo saboda aiyukan ta'addanci da har yanzu ya ke tafkwa a jihohin Benuwe da Nasarawa.

Ghana da yaransa sun kware wajen fashi da makami, garkuwa da mutane, kwacen motoci, da sauran miyagun aiyukan ta'addanci.

DUBA WANNAN: Buhari ya aika muhimmin sako zuwa AU, ECOWAS, da UN a kan juyin mulkin kasar Mali

Ogbode ya sanar da kotun cewa har yanzu rundunar 'yan sanda ta na gudanar da bincike a kan masu laifin tare da rokon a daga cigaba da sauraron karar domin rundunar 'ya sanda ta kara tattaro hujjoji.

Lauyan da ke kare wadanda ake kara, Barista Terhemen Oscar Aorabe, bai kalubalanci bukatar neman a daga cigaba da sauraron shari'ar ba.

Sai dai, ya sanar da kotun cewa zai rubuta takardar neman kotun ta sake zama domin sauraron bukatar neman bashi belin wadanda ya ke karewa.

Alkalin kotun ya daga zaman cigaba da sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba, 2020.

Nan take aka wuce da Honarabul Agbidye da Zuamo zuwa gidan kurkuku na tarayya da ke Makurdi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel