Katsina: Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke mutane biyu da dabbobin sata

Katsina: Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke mutane biyu da dabbobin sata

- Jami’an tsaro sun kama wasu mutane biyu dauke da dabbobin sata a Katsina

- Wadannan mutane sun karbi shanu daga ‘Yan bindiga za su saida a kasuwa

- Kakakin ‘Yan Sanda ya ce wadanda su ke zargin sun amsa laifinsu da kansu

Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Katsina sun kama wasu mutane da ake zargin su na taimakawa miyagun da su ke addabar Bayin Allah.

Jaridar Katsina Post ta ce jami’an tsaron sun yi ram da masu karbar dabbobin sata daga hannun ‘yan bindigan da su ke shiga kauyukan Katsina su na yin ta’adi.

Sakamakon wannan nasara da ‘yan sanda su ka yi, sun karbe dabbobi daga hannun wadanda ake zargi da agazawa ‘yan bindigan wurin yin gaba da dukiyar mutane.

Kakakin rundunar ‘yan sandnan jihar Katsina, Gambo Isah ya fitar da jawabi ya na cewa:

“A ranar 12 ga watan Agusta, 2020, da kimanin karfe 2:00 na rana bayan samun bayanai, dakarun SIB na jihar Katsina su ka yi nasarar kama wadannan mutane:

KU KARANTA: Alkaluma sun nuna duk ranar Allah sai an sace kusan mutum 4 a bana

Katsina: Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke mutane biyu da dabbobin sata
Gwamnan Katsina wajen sulhu da 'Yan bindiga
Asali: Twitter

(1) Abdullahi Saidu ‘Namiji’ mai shekara 40 daga Kauyen Gobirawa.

(2) Jafaru Aminu ‘Namiji’ mai shekara 50 daga Unguwar Nachibi.

Dukkansu daga garin Birnin Gwarim jihar Kaduna, dauke da shanun sata 12."

“A wajen binciken masu laifin, duka wadanda ake tuhuma sun amsa cewa sun karbi shanun daga ‘yan bindiga a karamar hukumar Faskari ta yankin Birnin Gwari.”

Gambo Isah ya ce wadannan mutane da aka kama, su na da niyyar saida dabbobin ne a kasuwa. “Bincike ya na cigaba da wakana.” Inji jami’in ‘yan sandan.

Dazu kun ji cewa ana zargin wata mata da cin amanar mijinta da farkarta a gidansa. Mai gidanta ya fadawa kotu cewa ta yaudaresa, ta kawo kato da sunan ‘Danuwanta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel