Garkuwa da mutane: Mazauna kauyukan Kaduna su na tserewa gudun hijira

Garkuwa da mutane: Mazauna kauyukan Kaduna su na tserewa gudun hijira

A lokacin da 'yan bindiga suka shiga Kwanar Farakwai ta karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a watan Yuni, suna da manufa. Kusan su 40 dauke da bindigogi suka nufa gidan Musa Ibrahim, wanda aka fi sani da Oga Musa.

Wurin karfe 1 ne kuma harbin bindigoginsu ya tada hankalin mazauna garin wadanda tuni suka gane cewa akwai matsala.

"Wurin 'yan bindiga 40 dauke da makamai suka fito dani daga gidana. A zatona kasheni za su yi, amma Ashe kudi suke bukata," Musa ya sanar da Daily Trust.

Musa ya ce sun ci gaba da buga mishi kofa, silin ya shige tare da boyewa amma yana addu'a. Sun duba duk wani lungu da sakon gidan suna neman shi.

Kamar yadda yace, ba su bi ta kan sauran iyalansa ba. Daga bisani suka ganshi sannan suka ja shi waje.

Musa ya sanar da yadda shi da wasu suka yi tafiyar sa'o'i 12 a daji inda suke zagaye da masu garkuwa da mutane. Bayan kwashe kwanaki 17 a maboyarsu, an biya Naira miliyan 4 a matsayin kudin fansa sannan aka sakosu.

Garkuwa da mutane: Mazauna kauyukan Kaduna su na tserewa gudun hijira
Garkuwa da mutane: Mazauna kauyukan Kaduna su na tserewa gudun hijira. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu a jihar Kano ta sake yanke wa wani hukuncin kisa

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, ayyukan masu garkuwa da mutanen ne yasa kauyukan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zaria suka fara tserewa zuwa birane. Sun ce masu garkuwa da mutanen suna zuwa da dare inda suke cin karensu babu babbaka.

"Masu dama suna komawa birane saboda masu garkuwa da mutane ko kuma tsoron nan gaba su za a sace," wani mai sarauta a yankin da ya bukaci a boye sunansa ya sanar.

Kwanar Farakwai na da nisan a kalla kilomita 50 daga garin Kaduna. Mazauna kauyen suna cewa masu garkuwa da mutane sun saba kutsawa suna sacesu. Ko bayan an sako su, suna rayuwa cike da tsoron sake sacesu.

"A Kwanar Farakwai kadai, fiye da iyalai 10 ne suka koma garin Kaduna, Zaria ko Rigachikun saboda sun sakankance cewa gwamnati ba za ta kawo musu dauki ba," Musa Ibrahim ya sanar.

Mazauna Kwanar Farakwai da Kamfanin Zangon Aya da yawansu manoma ne. Hakan ne yasa masu garkuwa da mutanen ke kallon masu kudin cikinsu suke kuma sacewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel