An bayyana dalilin da ya sa kasashen duniya su ka daina sayarwa da Najeriya makamai

An bayyana dalilin da ya sa kasashen duniya su ka daina sayarwa da Najeriya makamai

Wani mai nazarin harkokin tsaro kuma tsohon kwmishinan 'yan sanda (CP), Lawrence Alobi, ya ce kin sayarwa da Najeriya makamai da kasashen turai su ka yi ba zai rasa nasaba da rashin yarda da shugabancin kasa ba.

Yayin wata ganawarsa da jaridar Daily Trus a ranar Alhamis, Alobi ya ce daya daga cikin dalilan da ya sa aka daina sayarwa da Najeriya makamai shine; ''saboda shugabanninmu basu da kima".

Ya bayyana cewa duk da kasashen turai su na son yin kasuwancin sayar da makamai, su na duba makomar irin wannan kasuwanci saboda rashin tabbacin hannun da makaman za su fada bayan an sayesu.

Shi ma wani kwararre mai suna Ben Okezie, yayin tattaunawa da Daily Trust, ya bayyana cewa cin hancin da kasashen turai suka hango a Najeriya ne silar dakatar da sayar mu su makamai.

Ya bayyana cewa sun lura cewa makaman su na fadawa hannun balagurbin mutane a Najeriya, ya kara da cewa ya zama dole gwamnati ta farfado da mutuncinta ta hanyar karkade cin hanci.

A cikin makon jiya ne Daily Trust ta wallafa rahoton cewa babban kalubalen da yaki da ta'addanci ke fuskanta a Najeriya shine batun rashin isassun makamai.

An bayyana dalilin da ya sa kasashen duniya su ka daina sayarwa da Najeriya makamai
Sojojin Najeriya
Asali: Twitter

Kasar Amurka ce ta fara janye kafa daga sayarwa da Najeriya makamai bayan ta yi zargin cin zarafin fararen hula da dakarun soji ke yi.

DUBA WANNAN: Mun yi wa tufkar hanci, babu hukumar da za ta kara satar kudin gwamnati - Majalisa

Sai dai, a 'yan kwanakin baya bayan nan, Najeriya ta samu nasarar sayen wasu makamai daga kasashen gabashin turai da Asia ta wata hanyar cinikayya a tsakanin gwamnatoci.

Tuni gwamnatin tarayya ta fito ta roki manyan kasashen duniya da kar su yi la'akari da rahotanni da ake yadawa marasa tushe wajen daina sayarwa da Najeriya makamai.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuhumi shuwagabannin hukumomi da rundunonin tsaro kan yadda 'yan ta'adda ke samun makamai duk da cewa ya rufe bodar kasar.

Da yake jawabi a taron gwamnonin jihohi da shuwagabannin tsaro a ranar Talata a Abuja, ya nuna damuwarsa kan yadda 'yan ta'addan ke samun makaman da suke ta'addanci a kasar.

"Wadannan 'yan ta'addan suna rayuwa a cikin kauyuka. Amma me yasa makamansu basa karewa?" ya tuhumi shuwagabannin hukumomin tsaro da hafsoshin rundunar soji.

Taron ya kare da yin kira kan samar da dabaru na kawo karshen ta'addanci farat daya, yayin da jami'an tsaro zasu mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Taron ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro da yadda za a shawo kansu, inda aka nuna muhimmancin killace bayanan sirri domin karya lagon 'yan ta'addan.

Mahalarta taron sun nuna yakininsu na cewar idan aka sake samun yarda tsakanin jami'an tsaro da mutanen gari, to za a samu nasara wajen tattara bayanan sirri mai yawa kan 'yan ta'addan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel