Miyagun ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Majalisar Baraza/Dass, Hon. Mante Baraza

Miyagun ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Majalisar Baraza/Dass, Hon. Mante Baraza

Lamarin tsaro ya na kara tabarabarewa musamman a Arewacin Najeriya inda yanzu mu ka samu labarin kashe wani ‘dan majalisar dokoki.

Jaridar Leadership ta Najeriya, ta fitar da rahoto da safiyar Juma’a, 14 ga watan Agusta, 2020, cewa an hallaka wani ‘dan majalisar jihar Bauchi jiya.

Rahoton ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan Hon. Musa Mante Baraza sun kashe shi. Wannan mumman lamari ya auku ne a daren Juma’a.

Kafin mutuwarsa, Musa Mante shi ne mai wakiltar yankin mazabar Dass da Baraza a majalisar dokokin jihar Bauchi da ke Arewa maso gabashin kasar.

Wadannan miyagu da ake zargin cewa ‘yan fashi da makami ne, sun kuma dauke mai dakin marigayin, sun yi gaba da ita, a cewar jaridar.

KU KARANTA: Kasashen waje su ka hana Gwamnatinmu yakar ‘Yan ta’adda - Buhari

Miyagun ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Majalisar Baraza/Dass, Hon. Mante Baraza
Hon. Mante Baraza Hoto: Facebook/Bauchi Assembly
Asali: Twitter

Daga lokacin da wannan abu ya faru a ranar Alhamis cikin tsakar dare, babu wanda ya ji labarin inda matar ‘dan majalisar ta ke har zuwa yanzu.

A wani rahoton da ya fito daga Wikki Times, ana zargin cewa an sace wasu mutum uku daga cikin iyalin marigayi Musa Mante Baraza.

Kafin rasuwarsa, Honarabul Musa Mante Baraza, shi ne shugaban kwamitin sauraron korafi na majalisar dokokin jihar Bauchi.

Bayan haka Mante Baraza ya na cikin kwamitocin tattalin arziki da na harkar noma a majalisar.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Bauchi, DSP, Ahmed Mohammed Wakili ya tabbatar da wannan kisa, ya ce an sace mata biyu na ‘dan majalisar da ‘dansa.

Yanzu haka marigayin ya na kokarin murmurewa ne bayan kwanakin baya ya yi ta fama da cutar COVID-19. Ainihinsa mutumin garin Baraza ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel