Gwamna Ya Cika Alkwari, Ya Bude Kasuwar Zamani da Ta Lakume Naira Biliyan 2.98

Gwamna Ya Cika Alkwari, Ya Bude Kasuwar Zamani da Ta Lakume Naira Biliyan 2.98

  • Gwamna Ahmadu Fintiri ya ƙaddamar da sabuwar kasuwar Modibo Adama a Yola bayan sake ginata a kan Naira biliyan 2.98
  • Sabuwar kasuwar tana da shaguna 936 tare da kayan more rayuwa na zamani domin bunƙasa kasuwanci da da tattalin arzikin Adamawa
  • Fintiri ya ce bude wannan kasuwa zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga tare da samar da ingantaccen wurin kasuwanci ga ’yan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Adamawa - Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ƙaddamar da sabuwar kasuwar Modibo Adama da aka sake ginawa a garin Yola, a wani mataki na ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma haɓaka kuɗaɗen shigar da jihar ke samu.

An bai wa wani kamfanin gine-gine na cikin gida kwangilar sake gina kasuwar Yola a bara kan kuɗin da ya kai Naira biliyan 2.98.

Kara karanta wannan

Qatar ta ware kwanakin makoki, ta ba da hutun aiki bayan mutuwar tsohon Sarki

Gwamna Ahmadu Fintiri ya kaddamar da kasuwa a Adamawa Yola.
Kasuwar da Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya kaddamar a Yola. Hoto: @AdamawaLas79384
Source: Twitter

Sabuwar kasuwa mai shaguna 936

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin, Gwamna Fintiri ya ce aikin ya nuna yadda gwamnatinsa ke cika alƙawuran da ta yi wa al’umma, kamar yadda aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na intanet.

“Bara mun ziyarci wannan wuri, mun ga irin matsalar da ta faru, mun ji raɗaɗin asarar da aka yi, kuma muka yi alƙawarin ba wai kawai za mu sake gina kasuwar ba ne, har ma za mu samar wa ’yan kasuwa kasuwa ta zamani wadda ta dace da su,” in ji Gwamna Fintiri.

Ya ƙara da cewa sabuwar kasuwar Yola na daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar domin gano matsala tare da samar da mafita mai ɗorewa.

Fintiri ya ce aikin ya kuma tabbatar da cewa ’yan kwangilar cikin gida za su iya gudanar da manyan ayyuka idan aka ba su dama da kuma kyakkyawan kulawa.

An inganta tsaro da tsafta

Kara karanta wannan

A kula: Bauchi Jigawa da wasu jihohi 26 za su fuskanci ambaliyar ruwa

Ya ce an tsara aikin gaba ɗaya tare da kammala shi kashi 100 cikin 100 daga hannun ’yan kwangilar Adamawa inda sabuwar kasuwar ta ƙunshi shaguna 936, ciki har da rumfuna 120 da kuma shaguna 816 masu ƙofofi.

Haka kuma tana da katanga mai ƙarfi, manyan hanyoyin shiga motocin kashe gobara, tashar kashe gobara, tsarin samar da ruwa, rijiyoyin ruwa na sama, wuraren kashe gobara da kuma ingantattun wuraren tsafta.

Gwamnan ya ce sabuwar kasuwar ta maye gurbin tsohuwar kasuwar Yola wadda ta kasance mai cike da cunkoso, rashin tsafta da kuma yawan fuskantar gobara.

Gwamna Ahmadu Fintiri ya ce sabuwar kasuwar za ta bunkasa kasuwanci da kudaden shiga ga gwamnati.
Kasuwar Modibo Adama da Gwamna Ahmadu Fintiri ya kaddamar a Yola, jihar Adamawa. Hoto: @AdamawaLas79384
Source: Twitter

An magance matsalar gobarar baya

Ya bayyana cewa a baya ’yan kasuwa da mazauna yankin sun sha fama da gobara da ta rika lalata shaguna da kayayyaki masu darajar miliyoyin naira tare da jefa mutane cikin wahala.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Fintiri ya ce wasu mutane sun fara danganta matsalar gobarar da camfi maimakon duba hanyoyin da za a magance ta ta hanyar tsari da ingantattun matakai.

Ya ce gwamnatinsa ta magance matsalar gaba ɗaya ta hanyar sake gina kasuwar tare da saka kayan kariya daga gobara da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.

Kara karanta wannan

"Ku taimaka": Remi Tinubu ta roki Davido da sauran manyan mawaka a Najeriya

Gwamna Fintiri ya yi sauye sauye

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi garambawul a gwamnatinsa, inda ya sauya wurin aiki ga wasu kwamishinoni.

Ahmadu Umaru Fintiri ya bukaci kwamishinonin da abin ya shafa da su ci gaba da bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban Adamawa.

A cewar mai girma gwamna, sanarwar da aka fitar game da garambawul da Gwamna Fintiri ya yi, sauye-sauyen za su fara aiki ne nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com