Rikcin ADC: Ana Neman a Cafke Nafiu Bala da ke Son Rusa Tafiyar Atiku
- Jam'iyyar ADC ta nemi hukumar INEC ta mika Nafiu Bala Gombe ga hukumomin tsaro bayan ya yi karya kan samun lambar shiga shafinta
- Hukumar zabe ta INEC ta musanta ingancin takardar da Nafiu Bala ya fitar, ta tabbatar cewa ikirarin da ya yi ba gaskiya ba ne
- Kakakin ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ya rattaba hannu kan sanarwar da jam'iyyar ta fitar game da neman kana Nafiu Bala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Jam'iyyar adawa ta ADC ta fito da wata sanarwa tana neman a kama Nafiu Bala Gombe a kuma tuhume shi a gaban kotu.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar zabe ta INEC ta bayyana a fili cewa ikirarin da ya yi na samun damar shigar da sunayen 'yan takara don zabukan 2027 ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan
PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu

Source: Facebook
A cikin sanarwa kakakin ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a Facebook, jam'iyyar ta bayyana cewa matakin da Nafiu Bala ya dauka ya wuce gona da iri.
Neman kama Nafiu Bala
ADC ta yabi INEC kan yadda ta yi sauri ta fito ta musunta ikirarin Nafiu Bala, inda ta bayyana farin cikinta kan yadda hukumar ta bayyanar a sarari cewa takardar da Nafiu Bala ya yada ba ta gaskiya ba ce.
Jam'iyyar ta jaddada cewa lamarin ya wuce abin da ake iya ɗauka a matsayin wasa, ta ce zai iya tasiri a kan manyan cibiyoyin mulkin dimokuradiyya na ƙasar.
Jam'iyyar ta ce da mutum ya yi da'awar cewa ya samu hanyar shiga tsarin sirrin INEC na shigar sunayen 'yan takara, wannan yana haifar da damuwa mai nauyi da ya cancanci jan hankalin hukumomin tsaro.
ADC ta gargadi cewa idan aka yafe irin wannan aikin ba tare da gurfanar da mai laifi ba, wasu mutane na iya yin irin wannan kuskuren a nan gaba, wanda zai iya haifar da rikici da raunana amincin al'umma ga tsarin zaben kasar.

Kara karanta wannan
2027: Atiku ya kawo hujjoji, ya zargi Tinubu da naɗa wanda zai ruguza 'yan adawa a INEC

Source: Facebook
ADC ta kira shi ƙalubale ga INEC
Jam'iyyar ta fassara ayyukan Nafiu Bala Gombe a matsayin kalubale kai tsaye ga sahihancin INEC a matsayinta na hukuma mai gudanar da zabe.
ADC ta kara cewa yadda hukumomi za su yi martani kan lamarin zai aika da saƙo mai ma'ana ga dukkan waɗanda za su iya yi wa hukumomin gwamnati zagon ƙasa.
Jam'iyyar ta jaddada sadaukarwarta ga tsarin dimokuradiyya da mutunta cibiyoyi, tana mai kira ga hukumomin da suka dace su yi aiki da ƙarfin gwiwa don tabbatar cewa irin wannan karya ba zata zama al'ada a siyasar Najeriya ba.
Ikirarin da Nafiu Bala ya yi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Nafiu Bala da ke ikirarin zama halastaccen shugaban ADC ya ce ya daura sunayen 'yan takara a shafin INEC.
Hakan na zuwa ne yayin da jama'ar jam'iyyar ADC da dama ke sauraron matakin da za a dauka na sanya sunan Atiku Abubakar a shafin hukumar zabe.
Ana tsaka da haka ne Nafiu Bala da bai yarda da tafiyar su Atiku ba ya fitar da sunayen mutanen da ya ce su aka amince su yi wa ADC takara a 2027.
Asali: Legit.ng