Katsina: 'Yan bindiga sun sace 'yan mata 3 a sabon harin tsakar dare
A daren Lahadi, kungiyar 'yan bindiga da suka addabi jihar Katsina sun kai hari a yankin Saulawa da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar.
HumAngle ta gano cewa, kungiyar ta mamaye duk wasu wurare na karamar hukumar inda suka fara harbi babu kakkautawa. A hakan suka kutsa cikin gidaje da shaguna.
Majiyoyi da suka zanta da HumAngle sun tabbatar da cewa, kungiyoyin sun sace 'yan mata tare da barin wani mutum da manyan raunika.
Sun yi awon gaba da kayayyakin abinci da wasu abubuwan amfani wanda mallakin 'yan yankin ne.
"An ji harbe-harbe a ko ina a lokacin da nake kiran sallar Isha'i. Hakan yasa dole na daina kiran sallar bayan na ga wasu maza dauke da makamai suna shigowa yankin inda suke wakoki da ihu," mataimakin limamin masallacin Usman Hassan da ke yankin ya sanar.
"Sun wuceni inda kai tsaye suka fara shiga gidajen jama'a tare da kwashe musu kaya. Abinda na sani shine, sun yi garkuwa da mata uku sannan sun harbi wani mutum mai matsakaicin shekaru," ya kara da cewa.

Asali: UGC
KU KARANTA: Bukatu 4 da gwamonin arewa maso gabas suka mika ga FG
"Biyu daga cikinsu sun zo sun siya sigari. Daya daga cikinsu ya yi waya inda ya tambaya wa za su sace a yankin," wani mazaunin yankin mai suna Abba ya bayyana.
Abba ya kara da cewa yayi iyakar kokarinsu wurin kiran 'yan sanda amma bai samesu ba.
"Muna da lambobin kira na gaggawa kuma na kira ya fi sau biyar don bada rahoto amma basu dauka ba," yace.
Daya daga cikin 'yan matan da suka sace shekarunta 15 kuma diyar wani malami ce a kwalejin horar da malamai na yankin.
"Sun yi garkuwa da 'yar uwata Khadija wacce ta zo daga Dutsin-Ma don wani biki sannan sun harba Ibrahim," Fatima Aliyu ta jajanta.
"A halin yanzu bai san inda kansa yake ba, yana asibitin Kurfi don samun agaji," ta kara da cewa.
Wani mai arziki a yankin da ya zanta da HumAngle amma ya bukaci a boye sunansa, ya ce, "muna cikin mugun hali a yanzu maganar da nake muku. Mun tura 'yan sa kai don ceto 'yan matan."
'Yan matan biyu daga cikin wadanda aka sace sun tsero amma karamar har yanzu tana hannunsu, wata majiya ta kara da cewa.
Ya ce, "Yan mata biyun sun tsero lafiya kalau kuma mun kama uku daga cikin 'yan ta'addan. Daya yana asibiti yanzu amma biyu sun tsere da sassafe wurin karfe 2 na dare."
"Abinda ya bai wa kungiyar damar kawo mana hari shine rashin jami'an tsaro da za su yi martanin gaggawa. Sun dauka fiye da sa'o'i hudu kafin sun shigo cikin gidaje," ya kara da cewa.
Amma Abba yace, "abu mafi takaici shine yadda 'yan sanda suka musanta aukuwar lamarin tare da cewa ba a bai wa hukumarsu damar zuwa ba ko da sun ji harbin bindiga a ko ina."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng