Sace mutane 808 a 2020: Jihohin arewa hudu da aka fi garkuwa da mutane

Sace mutane 808 a 2020: Jihohin arewa hudu da aka fi garkuwa da mutane

- Wani rahoton bincike ya nuna cewa an yi garkuwa da jimillar mutane 808 a cikin watanni 6 na shekarar 2020

- Binciken jaridar Daily Trust ya gano cewa an kashe kimanin miliyan N96.4 wajen bawa ma su garkuwa da mutane kudin fansa a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na 2020

- Har yanzu babu wani hukunci takamaimai a kundin tsarin mulkin Najeriya domin hukunta laifin garkuwa da mutane

Babban birnin tarayya, Abuja, da jihar Katsina, gida ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun kasance a kasance a sahun farko na jihohin Najeriya da aka fi yawan yin garkuwa da mutane daga watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2020.

Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoton bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar kuma ta wallafa a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta.

Daily Trust ta bayyana cewa sakamakon bincikenta, wanda ta tattaro daga shafukan jaridu, ya nuna cewa an kashe kimanin miliyan N96.4 wajen bawa ma su garkuwa da mutane kudin fansa a tsakanin lokacin.

A yayin da aka yi garkuwa da jimillar mutane 22 a Kaduna, an yi garkuwa da mutane 19 a jihohin Katsina da Sokoto da kuma wasu mutane 18 a jihar Neja.

Sace mutane 808 a 2020: Jihohin arewa hudu da aka fi garkuwa da mutane
Wasu masu garkuwa da mutane da 'yan sanda suka kama a jihar Sokoto
Asali: Twitter

Idan aka kalli lissafin adadin mutanen da aka sace a kowanne wata, bincike ya nuna cewa an yi garkuwa da jimillar mutane 248 a watan Janairu, 130 a watan Tuli, da mutane 121 a watan Maris.

DUBA WANNAN: Mutuwar Janar Ismail Iliya: Buhari ya yi alhini, ya aika sako zuwa rundunar soji

Kazalika, an yi garkuwa da mutane 114 a wata Fabrairu, mutane 109 a cikin watan Yuni, mutane 45 a cikin watan Afrilu, da mutane 41 a cikin watan Mayu.

Jimillar lissafin ta nuna cewa an yi garkuwa da mutane 808 a sassan Najeriya daban-daban daga watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2020.

Duk da rundunar 'yan sanda ta sha kamawa tare da yin bajakolin daruruwan mutanen da aka kama da laifin yin garkuwa da mutane, har yanzu ba ta taba wallafa bayanai da adadin mutanen da aka zartarwa da hukunci ba.

Duk da kasancewar babu wani hukunci takamaimai da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada a kan laifin garkuwa da mutane, majalisun dokokin wasu jihohin sun amince da hukuncin kisa a kan laifin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel