An kashe 'yan bindiga biyu, an kubutar da mutane 15 a Katsina

An kashe 'yan bindiga biyu, an kubutar da mutane 15 a Katsina

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da cewa ta kashe wasu 'yan bindiga guda biyu tare da kubutar da mutane biyu da su ka sace a yankin karamar hukumar Dutsinma.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya aka rabawa manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne yayin da jami'an rundunar 'yan sanda a karkashin atisayen 'Puff Adder' su ka dira yankin bayan samun rahoton bullar 'yan bindiga dauke da bindigu.

A cewarsa, rundunar 'yan sanda ta samu labarin cewa 'yan bindiga dauke da bindigu samfurin AK 47 sun shiga kauyen Kwaro da ke yankin karamar hukumar Dutsinma a ranar 12 ga watan Agusta.

SP Isha ya kara da cewa 'yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Mohammed Auwal tare da sace wasu mutane biyu da dabbobi ma su yawa.

Kakakin ya bayyana cewa an yi musayar wuta a tsakanin 'yan bindigar da kuma jami'an rundunar 'yan sanda da su ka bi sahunsu a lokacin da su ke kokarin tserewa.

An kashe 'yan bindiga biyu, an kubutar da mutane 15 a Katsina
Gwamnan jihar Katsina yayin wani sulhu da 'yan bindiga a baya
Asali: Twitter

Ya ce jami'an rundunar 'yan sanda sun samu nasarar kashe biyu daga cikin 'yan bindigar yayin da sauran abokansu su ka gudu zuwa cikin daji tare da barin babur guda bakwai.

"Mun kubutar da mutane biyu; Musa Rabiu da Rabiu Sani, daga hannun 'yan bindigar ba tare da ko kwarzane ya samesu ba," a cewarsa.

DUBA WANNAN: NCDMB: Buhari ya bude katafaren ginin bene mai hawa 17 a Bayelsa (Hotuna)

Kazalika, ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta samu nasarar wani kwanson alburusan AK 47 guda daya da 'yan bindigar su ka jefar sakamakon matsin lambar da su ka fuskanta a wurin jami'an 'yan sanda.

SP Isha ya ce har yanzu jami'an 'yan sanda sun kewaye dajin da 'yan bindigar su ka shiga domin zakulo gawarwakinsu ko kuma kashesu idan suna raye.

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa nan bada dadewa ba za kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a wasu jihohin arewa maso yamma.

NAN

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel