CCTV ta raba gardamar zargin aikata fyaden da ake yi wa wani a Jihar Delta

CCTV ta raba gardamar zargin aikata fyaden da ake yi wa wani a Jihar Delta

Wani mutumi mai shekara 30 da aka bayyana sunansa a matsayin Jomaph ya shiga hannun ‘yan sandan jihar Delta bisa zargin yi wa wata yarinya fyade.

Jomaph ya shiga matsala ne bayan da na’urar CCTV mai daukar hoto ta fallasa shi zai yi lalata da karfin tsiya da wannan Baiwar Allah a garin Sapele, jihar Delta.

Jaridar Punch ta ce ana zargin an aikata wannan mummunan aiki ne a hanyar Oleh da ke garin Sapele a ranar Laraba da ta wuce da kimanin karfe 7:00 na safe.

Wannan yarinya mai shekaru 11 a Duniya ta shiga ban-daki ne, sai kwatsam aka ga ta fito ta na kuka, ta na cewa Jomaph wanda makwabcinta ne, ya yi mata fyade.

Ko da mutane su ka tuntubi Mista Jomaph, sai ya musanya wannan zargi, ya rantse cewa gaba daya bai sa idanunsa a kan wannan yarinya ba a safiyar wannan rana.

Makwabta sun lallabe shi ya amsa laifinsa idan da gaske bai dai gaskiya, amma ya tubure a kan bakarsa, har ma ya gayyaci ‘yan sanda su kama yarinyar da ‘yanuwanta.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun damke masu saidawa 'Yan bindiga dabbobi a Katsina

Wannan mutumi ya zargi yarinyar da ‘yanuwanta da laifin yi masa kazafi. Amma kuma na’urar CCTV da wani makwabcinsu ya daura, ya nuna ainihin abin da ya auku.

Da aka bibiyi na’urar ta CCTV, an ga takin Jomaph zuwa cikin kewaye jim kadan bayan wannan yarinya ta shiga ban dakin. Jaridar ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Yayin da ‘yan sanda su ka gayyaci yarinyar da iyayenta domin yi masu tambayoyi ne sai wannan makwabci ya kai wa jami’an tsaro hotunan CCTV na abin da ya faru.

Kakakin ‘yan sanda ta jihar Delta, Onome Onowhakpoyeya, ta tabbatar da wannan lamari. Jami’ar ta ce yanzu ‘yan sanda sun kama wannan matashi da ake zargi da laifi.

“Lamarin gaskiya ne, kuma an kama matashin bayan an samu hujjojin CCTV da ke nuna ya kutsa cikin ban-dakin tare da yarinyar, ana kan bincike.” Inji Onowhakpoyeya

Da zarar an kammala wannan bincike, za a mika maganar zuwa ofishin CID da ke Asaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng