‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa

‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa

- Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai farmaki wani kauye a jihar Yobe

- Sun shiga garin Mashio da ke karamar hukumar Fune sannan suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka sace hakimin kauyen, Isa Mai Buba da dansa

- Lamarin ya afku ne a daren ranar Asabar, sai dai dan hakimin kauyen ya yi nasarar tserewa a safiyar ranar Lahadi amma har yanzu mahaifinsa na kame

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne sun kai farmaki wani kauye a jihar Yobe.

Maharan sun shiga garin Mashio da ke karamar hukumar Fune sannan suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka sace hakimin kauyen, Isa Mai Buba da dansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, da kuma mukaddashin shugaban karamar hukumar da abun ya shafa, Abubakar Kolere sun tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talbijin din Channels.

Sun yi bayanin cewa lamarin ya afku ne a daren ranar Asabar, inda ya bayyana cewa dan hakimin kauyen ya yi nasarar tserewa a safiyar ranar Lahadi amma har yanzu mahaifinsa na kame.

‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa
‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa Hoto: The Eagle Online
Asali: UGC

Harin na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sun kai wa mutum 14 hari a kauyen Ukuru da ke karamar hukumar Mariga na jihar Neja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Abiodun Wasiu ya tabbatar da harin da adaadin mutanen da suka mutu a wani jawabi.

Amma wani mazaunin garin, Musa Audu, wanda ya shaidi harin, ya bayyana abunda ya wakana ga Channels TV a wayar tarho.

Ya yi bayanin cewa ‘yan bindiga sun kai mamaya garin a lokacin da mambobin kungiyar ‘yan banga suka fita sintiri a wasu jejin da ke yankin.

Audu, wanda dan uwansa ya kasance cikin wadanda ‘yan bindiga suka kashe, ya bayyana cewa harin ya afku ne a lokacin da ake cin kasuwar Mariga wanda ya samu haalartan ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Abubuwa 3 da suka hana cutar yin tasiri a Afrika

Ya ce an tsinci gawawwakin mutum 15, inda ya kara da cewar mutane da dama sun ji raunuka yayinda suke tserewa jejin da ke kusa kuma har yanzu ana kan nemansu.

A halin da ake ciki, kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa rundunar na kokarin ceto basaraken.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel