Garkuwa da mutane ya zama sabon salon Miyagu na samun miliyoyin kudi

Garkuwa da mutane ya zama sabon salon Miyagu na samun miliyoyin kudi

Wani bincike mai tada hankali ya nuna akalla ba a kasara ba, an sace mutane 800 a cikin kasar nan daga farkon wannan shekara zuwa watan jiya.

Jaridar Daily Trust ta yi wani bincike na musamman, inda ta gano cewa mutane 808 ake da labarin an yi garkuwa da su a fadin kasar nan daga Junairu zuwa Yuli.

Tsakannin watannin nan bakwai, jaridun Najeriya sun fitar da rahoton garkuwa da mutane na wannan adadi, aka kuma bukaci a biya fansar Naira biliyan 4.2

Ko da ba a biya dukkanin kudin fansar da aka bukata ba, amma ana da tabbacin cewa masu wannan ta’adi sun tashi da kusan Naira miliyan 100 a cikin shekarar nan.

Rahoton ya ce abin da ya shiga hannun masu garkuwa da mutanen ya haura Naira miliyan 96. Akwai wasu dubunnan mutanen da aka sace ba tare da an ji labari ba.

Garkuwa da mutane shi ne babban barazanar da mutanen Najeriya da baki su ke fuskata a yau. Shekaru kafin yanzu a Kudancin kasar nan kadai ake wannan danyen aiki.

Jihohin da aka samu labarin satar mutane daga Junairu zuwa Yuli sun hada da Abia, Adamawa, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Borno, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, da jihar Filato.

KU KARANTA: Matan da su ka shiga hannun Boko Haram sun bada labarin Sambisa

Garkuwa da mutane ya zama sabon salon Miyagu na samun miliyoyin kudi
Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare Hoto: NPF
Asali: Twitter

Jaridar ta ce sauran jihohin su ne: Enugu, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kogi, Kuros-Riba, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Wannan barna bai tsaya a wadannan jihohi 32 ba, ya shiga har babban birnin tarayya Abuja.

A jihar Delta (14) ne lamarin ya fi kamari, sai kuma jihar Ondo (11). Daga nan sai Edo (10), Kuros-Riba (9). Yankin Arewa ta tsakiya ne ya zo na biyu a jerin bayan shiyyar Neja-Delta.

Yankin Arewa maso yamma ya zo na uku kamar yadda Alkaluma su ka nuna. A jihar Katsina kadai an yi garkuwa da mutane akalla 17 a cikin watanni bakwai na farkon bana.

Da labarin satar mutane 16, yankin Arewa maso gabas ne na gaba a sahun. Shiyyoyin Kudu maso gabas da Kudu maso yamma su ne su ka zo karshe a jerin da mutum 14 da 9.

A 1992, mutum daya aka samu labarin an yi garkuwa da shi. Daga 1993 zuwa 1996, babu wanda aka yi garkuwa da shi a Najeriya. A 1997 da 1998 an samu labarin garkuwa da mutum 8.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel