Rashin tsaro: Gwamnan Nasarawa ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa

Rashin tsaro: Gwamnan Nasarawa ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule a ranar Talata ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja sakamakon hauhawar rashin tsaro a jihar.

Sule ya sanar da manema labaran gidan gwamnati cewa jihar Nasarawa ta kasance a kanun labarai a cikin kwanakin nan saboda tsanantar garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Ya tunatar da yadda a cikin kwanakin nan aka kashe wani basarake a jihar.

Gwamnan ya danganta kalubalen tsaron da ya addabi jihar da ayyukan 'yan bindiga wadanda suka shiga yankin daga arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Ya ce 'yan bindigar na amfani da tsaunikan jihar wurin samun buya.

Sule ya ce wasu mafarauta da kungiyoyin 'yan sa kai sun tashi don tarar wannan kalubalen.

Rashin tsaro: Gwamnan Nasarawa ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa
Rashin tsaro: Gwamnan Nasarawa ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Ya ce, "Mafarauta a jihar tare da wasu kungiyoyin 'yan sintiri a Nasarawa ne suke bibiyar lamarin saboda sun san yanayin yankin.

"Yan ta'adda a jihar Nasarawa baki ne, ba 'yan jihar bane. Saboda haka, jama'ar mu sun san su kuma za a iya bibiyarsu.

"Wasu 'yan bindiga daga yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas sun shiga suna amfani da tsaunikan jihar don buya.

"Su ne ke shiga kauyuka da birane suna sace mutane tare da garkuwa da su. Muna fuskantar hauhuwar fashi da makami."

KU KARANTA KUMA: Buhari ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan tada tarzoma

Gwamnan ya bayyana cewa da goyon bayan jami'an tsaro a jihad, kalubalen tsaro zai zama tarihi.

Ya ce yana godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa makaranta ta uku ta horon hafsin 'yan sanda a jihar Nasarawa, bayan wadanda aka kafa a Borno da Osun.

A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun yi garkuwa da 'ya'yan tsohon kwamishina a jihar Zamfara, Bello Dankande, da wasu mutum biyu da suka hada da jami'an NSCDC.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya sanar da hakan a wata takardar da ya bai wa manema labarai a Gusau.

Ya ce an kashe mutum daya kuma wani ya ji miyagun raunika.

Ya ce lamarin ya faru ne a gidan tsohon kwamishinan kananan hukumomi da al'amuran masarautun da ke Gamji a karamar hukumar Bakura ta jihar a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel