Soke Zabubbukan ADC: Atiku Ya Aika Sako ga Magoya Bayan Jam'iyyar kan Zaben 2027
- Atiku Abubakar ya ce hukuncin Kotun Daukaka Kara bai soke zaben fidda gwani na ADC don zaben 2027 ba
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi wasu da yada bayanan da ba su dace ba domin raunana 'yan adawa
- Ya ce jam'iyyar za ta daukaka kara zuwa Kotun Koli tare da bukatar magoya baya su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci mambobin jam'iyyar ADC da miliyoyin 'yan Najeriya masu fatan ganin sauyin dimokuradiyya na gaskiya su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da kasancewa masu jajircewa.
Atiku ya ce sabanin bayanan da ake yadawa a wasu bangarori, Kotun Daukaka Kara ba ta soke zaben fidda gwani da jam'iyyar ADC ta gudanar domin tsayar da 'yan takararta a zaben shekarar 2027 ba.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.
Atiku ya yi martani kan hukuncin
Atiku ya bayyana cewa kokarin bayyana hukuncin kotun a matsayin karshen tikitin takarar shugaban kasa na ADC wani bangare ne na ci gaba da yada bayanan da ba su dace ba domin raunana 'yan adawa da kuma rikitar da 'yan Najeriya.
"Masu murnar wannan hukunci a yau su yi murna cikin taka-tsantsan. Wadanda kuma ke kokarin sayar wa magoya bayansu fata na karya su tuna cewa farfagandar siyasa ba za ta taba maye gurbin hukuncin kotu ba."
- Atiku Abubakar
"Hukuncin ya shafi zaben shugabannin jihohi ne"
Atiku ya ce hukuncin da ake magana a kai ya shafi yadda aka gudanar da zaben shugabannin jam'iyya a jihohi da kuma wa'adin kwamitocin zartarwa na jihohi.
A cewarsa, babu wani abu a cikin bayanan hukuncin da ke nuna cewa kotu ta soke zaben fidda gwani da ADC ta gudanar bisa tanadin dokar zabe.
Ya kara da cewa akwai babban bambanci a doka tsakanin zaben shugabannin jam'iyya ta hanyar tarurrukan cikin gida da kuma zaben fidda gwani na tsayar da 'yan takara.
Atiku ya yi magana kan hukuncin kotu
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce doka ta tanadi cewa kotu tana yanke hukunci ne kan batutuwan da aka gabatar mata kawai.
Ya ce ba ta kirkirar sababbin takaddama ko yanke hukunci kan abubuwan da ba a gabatar mata ba, rahoton jaridar Daily Trust ya nuna hakan.
Atiku ya kuma zargi abokan hamayyarsa da fifita yada fassarar hukunci a kafafen sada zumunta maimakon karanta abin da kotu ta yanke.

Source: Twitter
ADC za ta garzaya Kotun Koli
Atiku ya bayyana cewa suna mutunta bangaren shari'a, kuma sun umarci tawagar lauyoyinsu da su daukaka karar zuwa Kotun Koli domin samun hukunci na karshe kan batutuwan da suka taso daga hukuncin Kotun Daukaka Kara.
Dan takarar shugaban kasar na ADC a zaben 2027 ya ce suna da cikakken yakini da tsarin shari'ar Najeriya.
A karshe, Atiku ya ce:
"Hanyar zuwa zaben 2027 tana nan a bude, kuma ba wata farfaganda da za ta iya dakile kudurin 'yan Najeriya na ganin an samu kasa mafi kyau. Manufarmu ba ta canza ba, kuma da yardar Allah da kuma zabin 'yan Najeriya, za mu cimma burinmu."
Atiku ya soki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki shugaban kasar Bola Tinubu.
Atiku ya bayyana takaici a kan matakin da Bola Ahmed Tinubu ya dauka bayan ceto dalibai 44 da aka sace a jihar Oyo a matsayin gazawar shugabanci.
Asali: Legit.ng


