Manyan Labarai A Yau
Kwamandan Operation Hadin Kai da ke yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, Manjo Janar Christopher Musa, ya ce yan Boko Haram fiye da 60,000 ne suka mika wuya.
Tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai, ya ce bai da alaka da kayayyakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kwace kwanan nan a Abuja.
Dakarun Operation Safe Haven sun dakile yi nasarar dakile wani hari da yan bindiga suka kai garin Gajin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.
Wata kungiya ta roki jam'iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, da su yi watsi da shirin gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.
Wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun kaddamar da hare-hare kan manoma a yankin gabashin jihar Sokoto. Sun kashe manoma 11 a gonakinsu.
Fusatattun mambobin PDP a ranar Lahadi, sun mamaye sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri don hana dakataccen shugaban jam’iyyar reshen jihar Borno shiga ciki.
Rabiu Kwankwaso ya ce akwai ‘yan hanna ruwa gudu a LP. Kwankwaso ya bayyana matsalarsa da Peter Obi da yankin da zai fito da abokin takararsa a Jam’iyyar NNPP
Rundunar sojojin sama tare da taimakon rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta kashe wasu mayakan ISWAP masu yawan gaske a karamar hukumar Marte da ke jihar Borno.
Kwararrun likitoci sun bayyana cewa direbobin da ke tafiya mai nisa wadanda yayan marainansu kan dauki zafi na cikin hadarin kamuwa da matsalar karancin maniyi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari