Direbobi masu dogon tafiya na iya fuskantar karancin maniyyi, Masana sun yi gargadi

Direbobi masu dogon tafiya na iya fuskantar karancin maniyyi, Masana sun yi gargadi

  • Likitoci sun yi kakkausar gargadi ga direbobin manyan motoci masu dogon tafiya ba tare da na'urar sanyaya mota ba
  • A cewar wasu masana kiwon lafiya, wadannan direbobi na iya kamuwa da matsakar karancin maniyyi
  • Hakan na faruwa ne sakamakon zafin da yayan marainarsu kan dauka sakamakon zama kan injin mota

Kwararrun likitoci sun bayyana cewa direbobin da ke tafiya mai nisa wadanda yayan marainansu kan dauki zafi na cikin hadarin kamuwa da matsalar karancin maniyyi.

A cewar likitocin, yayan maraina na bukatar su kasance da sanyi fiye da jiki domin samar da maniyyi, kuma zama na tsawon lokaci a kansu na iya kawo karancin maniyyi ga da namiji.

Tireloli
Direbobi masu dogon tafiya na iya fuskantar karancin maniyyi, Masana sun yi gargadi Hoto: PM News
Asali: UGC

Sun ce cututtukan da ba a magance ba, rashin gwaje-gwaje, tiyata, barasa, muhalli da salon rayuwa na iya shafar ingancin kwayoyin maniyyin da namiji.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Wani likita a asibitin Ogah da ke Gugar, jihar Edo, Dr Gabriel Ogah, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ga direbobi masu dogon tafiya wadanda ke zama a motocin da basu da na’urar sanyaya wuri na tsawon awanni da dama, kamar direbobin tirela, akwai yiwuwar su kasance da karancin maniyyi.
“Zafin injin manyan motoci na iya shafar yayan maraina idan suka yi kusa da injin din. Wasu lokutan, idan ka zauna a bayan direba, za ka ga cewa akwai zafi, toh ka yi tunanin yaya ga direban da ke zaune kan injin; zafin injin na iya kashe kwayoyin maniyyi.”

Hakazalika, wani likitan mata, Dr Joseph Akinde, ya ce zafin manyan motoci na iya haifar da yin lahani ga maniyyi, jaridar Punch ta rahoto.

Sai dai kuma, kwarru sun bayyana cewa maza masu karancin maniyyi na iya yiwa mace ciki.

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

Wani kwararren likitan mata a asibitin koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Nnewi, Dr Stanley Egbogu, ya ce:

“Idan mutum yana da karancin maniyyi, kafin yanzu, yana da matukar wahala mutum ya yiwa mace ciki. Don haka, abin da muke yi yanzu shine maida hankali ga maniyyi. Muna wanke matattun don shirya maniyyi sannan mu sanya mashi kuzari. Akwai wasu sinadarai da muke karawa wadanda suke raye don su sa su saurin ninkaya; har ma wadanda ke shirin mutuwa, muna sa su saurin ninkaya.”

A cewarsa, maganin karancin maniyyi ya danganta da abun da ya haddasa shi ne.

Yadda masu ciwon suga za su yi azuminsu cikin sauki

A wani labarin kuma, wani kwararren likita mai suna Dr. Oluwarotimi Olopade, ya bukaci masu ciwon sukari na 2 da ke fatan yin azumi da su tattauna da likitocinsu kafin su fara.

Wannan kira na Dr Olopade na zuwa ne a daidai lokacin da watan Ramadana ke kara karatowa, wanda a cikinsa Musulmi ke yin azumi na kwanaki 29-30.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Likitan wanda ya kuma kasance masanin ciwon suga a asibitin koyarwa na jami’ar Lagas, ya bayyana cewa akwai bukatar masu ciwon suga su zanta da likitocinsu don sanin ko sun cancanci yin azumi bisa ga matsayin lafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel