Dakarun sojoji sun dakile harin yan bindiga a jahar Plateau

Dakarun sojoji sun dakile harin yan bindiga a jahar Plateau

  • Dakarun rundunar Operation Safe Haven sun dakile wani harin yan bindiga a garin Gajin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Plateau
  • Maharan sun yi yunkurin kaddamar da harin ne a safiyar yau Litinin, 4 ga watan Yuli, amma sai yan banga suka fuskance su kafin zuwan sojoji
  • Kakakin rundunar Operation Safe Haven a Jos, Ishaku Takwa, ya tabbatar da lamarin inda ya ce yan ta'addan sun tsere a lokacin da suka hango su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau - Rundunar Operation Safe Haven a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli, sun dakile wani hari da yan bindiga suka kai garin Gajin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.

Mazauna garin sun fadama jaridar Premium Times cewa an kai masu farmaki ne a safiyar ranar Litinin, 4 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani basarake a Plateau, sun kashe dansa

An tattaro cewa a lokacin da yan bindigar suka isa kauyen, sai yan kungiyar yan banga suka tunkare su na tsawon mintuna kafin isowar dakarun sojoji.

Sojoji
Dakarun sojoji sun dakile harin yan bindiga a wata jahar arewa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Kakakin rundunar Operation Safe Haven (OSH) Jos, Ishaku Takwa ya fada ma jaridar cewa maharan sun tsere lokacin da dakarun sojin suka iso garin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manjo Takwa ya ce:

“Mun samu rahoto daga mazauna yankin cewa bayan mun dakile harin, an gano gawarwakin mutane takwas wanda jami’anmu basu tabbatar ba.
“Na kira kwamandan yankin don tabbatarwa, ya ce dakarun basu ga kowani gawa ba, don haka ba za mu iya tabbatar da abun da bamu gani ba.”

Ya yi bayanin cewa dakarunsu na da sansanoni hudu a karamar hukumar Wase don haka, suna nan a koda yaushe, basu taba janyewa ba kuma ba za su iya barin bakin ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

Ana ta samun karuwar hare-haren yan bindiga a Plateau da jihohin da ke makwabta.

Kwanaki wasu yan bindiga sun fadama mazauna garuruwan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwan Tsohon Soldier, Anguwan Yuhana da Anguwan Mangu da su bar gidajensu ko kuma a kar masu farmaki.

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, Ado Buba, shugaban karamar hukumar Wase, ya ce yana kan hanyar tafiya don haka ba zai iya magana.

Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe manoma 11 a Sokoto

A wani labari na daban, mun ji cewa yan fashi da makami a yankin gabashin jihar Sokoto sun kaddamar da kazaman hare-hare kan manoma, jaridar The Nation ta rahoto.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kashe manoma 11 a cikin makon da ya gabata a garin Gandi Dalike da ke yankin karamar hukumar Rabah ta jihar.

Wani mazaunin yankin ya ce yan bindigar da yawansu sun farmaki kauyen a ranar Asabar, 2 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 8, wata ‘Yar Chibok ta kubuta daga hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram

Asali: Legit.ng

Online view pixel