'Ni Fa Ban Yi Wannan Alkawari ba': Minista kan Kawo Sauyi a Wutar Lantarki

'Ni Fa Ban Yi Wannan Alkawari ba': Minista kan Kawo Sauyi a Wutar Lantarki

  • Ministan makamashi a Najeriya, Joseph Tegbe ya yi karin haske kan yada wasu jita-jita game da gyaran wutar lantarki a kasar
  • Ministan ya yana magana ne kan rahoton cewa ya yi alkawarin gyara matsalar lantarkin Najeriya cikin watanni uku yayin tantance shi
  • Kakakinsa Adeola Adelabu ya ce Tegbe ya ce za a fara gyaran farko cikin kwanaki 100, amma manyan sauye-sauye za su dauki shekara guda

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan makamashi a Najeriya, Joseph Olasunkanmi Tegbe ya fara aiki a matsayin sabon minista bayan tantance shi.

Sai dai musanta rahotannin cewa ya yi alkawarin gyara tsarin lantarkin Najeriya cikin watanni uku kacal.

Minista ya ƙaryata rahoton da ake yaɗawa kan gyaran wutar lantarki
Sabon ministan makamashi, Joseph Tegbe a Abuja. Hoto: Joseph Olasunkanmi Tegbe.
Source: Instagram

Sanarwar da Adeola Adelabu ya wallafa a shafin X ta ce Tegbe bai taba yin irin wannan alkawari ba, domin har yanzu ana tattaunawa kan jadawalin gyaran.

Kara karanta wannan

Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki

Minista ya ƙaryata gyara wuta a wata 3

Ta bakin Adelabu, Tegbe ya ce an karkatar da abin da ya fada yayin tantancewarsa a Majalisar Dattawa ranar 6 ga Mayu, 2026.

Adelabu ya bayyana cewa Tegbe ya fada wa sanatoci cewa za a fara matakan farko na daidaita tsarin lantarki cikin kwanaki 100 na farko.

Sai dai ya ce manyan sauye-sauyen tsarin lantarki da ake bukata domin samar da ingantaccen wuta a kasar za su iya daukar kusan shekara guda.

Ya ce gyaran zai mayar da hankali wajen dawo da martabar bangaren lantarki, magance matsalar iskar gas da kuma kara yawan mita a gida-gida.

Ministan makamashi ya yi magana game da wutar lantarki
Shugaba Bola Tinubu da sabon ministan makamashi, Joseph Tegbe. Hoto: @StateHouse/x.
Source: UGC

Abin da Tegbe ya ce yayin tantance shi

A yayin tantancewar, Tegbe ya shaida wa sanatoci cewa ‘yan Najeriya za su fara ganin canji mai kyau a bangaren lantarki cikin lokaci mai zuwa.

Har ila yau, ya yi alkawarin tabbatar da daidaiton tsarin lantarki, sabunta kayan aiki da kuma tabbatar da gaskiya a bangaren samar da wuta.

Kara karanta wannan

Kashe ministan taron Mali ya rikita Najeriya, ta kawo mafita kan ta'addanci

Kan batun kudin lantarki kuwa, Tegbe ya ce sauye-sauyen da gwamnati za ta yi ba za su cutar da talakawa masu rauni ba.

Sanarwar ta kara da cewa Tegbe yana maraba da tattaunawa mai anfani da kafafen yada labarai tare da tabbatar da gaskiya wajen gudanar da aikinsa.

Shugaba Bola Tinubu ne ya nada Tegbe a matsayin ministan lantarki bayan sauyin majalisar ministoci da ya sa tsohon minista Adebayo Adelabu ya bar mukaminsa.

Tegbe, wanda injiniya ne kuma masani kan manufofin gwamnati, ya bayyana shirinsa na magance matsalolin faduwar lantarki da karancin kayan samar da wutar lantarki.

Matsalar lantarki ta farko a 2026

Mun ba ku labarin cewa babban tushen samar da wutar lantarki a Najeriya ya durkushe, lamarin da ya jefa 'yan kasa a cikin duhu a ranar Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2026.

Rahotanni sun nuna cewa zuwa karfe 1:00 na rana, babu wani kamfanin raba wuta da ya mu ko digo daga babban tushen samar da wuta na kasa.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan matsala a 2026, duk da dai an sha fama da lalacewar wuta a shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.