Sojoji sun ragargaji mayakan ISWAP, sun aika da dama lahira

Sojoji sun ragargaji mayakan ISWAP, sun aika da dama lahira

  • Dakarun sojoji sun ragargaji mayakan ISWAP wani farmaki da suka kai ta sama a yankunan Sabon Tumbun da Jibularam a karamar hukumar Marte ta jihar Borno
  • Sojojin tare da hadin gwiwar jami'an MNJTF sun kashe mayakan da dama a harin da suka kai a ranar Juma'a
  • Sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa mayakan suna ta haduwa su da yawa a yankin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Jaridar The Cable ta rahoto cewa rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta kashe wasu mayakan ISWAP a jihar Borno.

Dakarun MNJTF na gudanar da ayyukansu ne a kasashen Chadi, Kamaru da kuma Najeriya.

Jahar Borno
Sojoji sun ragargaji mayakan ISWAP, sun aika da dama lahira Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cewar Zagazola Makama, masani kan al'umar tsaro a tafkin Chadi, harin da sojoji suka kai ta sama ne ya kashe mayakan na ISWAP a ranar Juma’a a Sabon Tumbun da Jibularam a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro: 'Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 4,770 sun mika wuya cikin makwanni 2

Majiyoyi sun ce aikin ya biyo bayan samu bayanan sirri da ke nuna cewa mayakan ISWAP suna ta haduwa su da yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta nakalto majiyar na cewa:

“Binciken bayan fafatawar ya nuna cewa harin saman ya yi tasiri sosai domin an kashe mayakan ta’addanci da dama, yayin da wasu suka ji mummunan rauni.
“Ba za mu iya tabbatar da adadin yan ta’addan da aka kashe ba, amma sun fi dozin daya.”

Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani basarake a Plateau, sun kashe dansa

A wani labarin, tsagerun yan bindiga sun farmaki garin Angwan Baraya da ke masarautar Pyem, karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau inda suke ta harbi kan mai uwa da wahabi.

A yayin harin wanda ya afku a safiyar Lahadi, 3 ga watan Yuli, yan bindigar sun raunata hakimin garin, Baba Yarima Jabil sannan suka harbe dansa mai suna Chamsan har lahira.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Hakazalika, maharan sun yi awon gaba da matar hakimin da kuma wata kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel