Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe manoma 11 a Sokoto

Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe manoma 11 a Sokoto

  • Tsagerun yan bindiga sun kai farmaki kan manoma a yankin gabashin jihar Sokoto a ranar Asabar, 2 ga watan Yuli
  • An tattaro cewa yan bindigar sun kuma hallaka manoma 11 da ke kan gudanar da ayyuka a gonakinsu
  • Mummunan harin ya afku ne a yankin garin Gandi Dalike da ke karamar hukumar Rabah ta jihar

Sokoto - Yan fashi da makami a yankin gabashin jihar Sokoto sun kaddamar da kazaman hare-hare kan manoma, jaridar The Nation ta rahoto.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kashe manoma 11 a cikin makon da ya gabata a garin Gandi Dalike da ke yankin karamar hukumar Rabah ta jihar.

Yan bindiga
Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe manoma 11 a Sokoto Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin ya ce yan bindigar da yawansu sun farmaki kauyen a ranar Asabar, 2 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo

Sakataren hakimin Gandi, Alhaji Tukur Muhammad, ya ce maharan sun isa yankin da maraicen wannan rana sannan suka kashe wasu manoma a gonakinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma kawo cewa wani jigo a Gandi, Alhaji Idris Gandi, ya ce yan bindiga sun kashe wasu manoma hudu da ke aiki a gonakinsu a Gidan Buwai da ke kauyen Gandi a kwanan nan.

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo

A wani labarin, mun ji cewa wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu limaman cocin Katolika biyu a jihar Edo.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan masu garkuwa da mutane sun kashe wani limamin Katolika mai suna Christopher Odia a jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani basarake a Plateau, sun kashe dansa

A ranar Asabar, 2 ga watan Yuli ne aka yi garkuwa da limaman, Rev fr. Uboh Philemon na St. Joseph Retreat Centre da Rev. Fr. Udoh Peter na St. Patrick’s Catholic Church, Uromi dukkansu a Ugbokha, karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel