Yakin Iran da Isra'ila: An 'Gano' Kasar da Tafi Cin Moriyar Rikicin fiye da Amurka
- Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasa a Amurka, Kamala Harris ta yi magana game da yakin Iran da Isra'ila
- Harris ta zargi Donald Trump da taimaka wa Vladimir Putin ta hanyar sassauta takunkumin Rasha yayin rikicin Iran da ake fama da shi yanzu
- Ta ce gwamnatin Trump tana karkatar da makamai da kariyar sama daga Ukraine zuwa Gabas ta Tsakiya saboda tashin hankalin Iran mai ƙaruwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta soki shugaban ƙasa, Donald Trump a yakin Iran.
Kamala Harris ta caccaki Trump kan yadda yake tafiyar da rikicin Iran da ake fama da shi yanzu wanda kasar Rasha ke cin gajiya.

Source: Getty Images
Ƙasar da tafi cin ribar yakin Iran
Harris ta ce Rasha da shugaba Vladimir Putin ne suka fi cin moriyar rikicin saboda sauye-sauyen manufofin Amurka da suka shafi takunkumi da harkokin soja, cewar Fox News.
Yayin wani taron jama'a da aka gudanar, Harris ta bayyana cewa gwamnatin Trump tana raunana Ukraine tare da ƙarfafa Moscow ta hanyar sassauta takunkumin tattalin arziki da aka kakaba wa Rasha.
Ta ce hakan ya bai wa Rasha damar sake samun kuɗaɗe daga sayar da man fetur duk da matsin lambar ƙasashen yamma.
Harris ta ce:
"Kun san waye ne babban wanda yake cin nasara daga yakin Iran? Rasha.”
Ta ƙara da cewa sassauta takunkumi ya taimaka wa Moscow wajen sayar da man fetur da aka hana ta kasuwancinsa saboda yakin Ukraine da aka dade ana yi.
Ta kuma bayyana cewa wasu makamai da kayan kariyar sama da ya kamata a tura Ukraine yanzu ana kai su Gabas ta Tsakiya saboda rikicin Iran.
Harris ta ce wannan mataki yana raunana ƙawayen Amurka tare da ƙarfafa tasirin Putin a yankin Turai ta Gabas.

Source: Getty Images
Yan Democrats sun taso Amurka a gaba
Jam’iyyar Democrats ta dade tana zargin cewa rage tallafin da Amurka ke bai wa Ukraine zai taimaka wajen ƙara ƙarfin Rasha da kuma barazana ga ƙungiyar NATO.
A cewarsu, yakin Ukraine muhimmin gwagwarmaya ne tsakanin ƙasashen dimokuraɗiyya da gwamnatocin kama-karya.
Sai dai ‘yan Republican sun kare matakan Trump kan Iran, inda suka ce ƙarfafa rundunar sojin Amurka zai taimaka wajen kare muradun ƙasar da dawo da daidaito a duniya bayan rikice-rikicen da suka ƙaru a ƙasashen waje.
Rahoton ya kuma tuna da kalaman da Putin ya yi a lokacin zaɓen shugaban Amurka na 2024 lokacin da ya nuna yana son Kamala Harris ta jagoranci Amurka maimakon Trump.
Wannan magana ta jawo suka daga ‘yan Republican da suka ce Democrats sun raina muhimmancin furucin shugaban na Rasha, cewar rahoton Meaww.com.
Rasha da Ukraine sun sanar da tsagaita wuta
Mun ba ku labarin cewa shugabannin kasashen Rasha da Ukraine sun sanar da tsagaita wuta a yakin da suka shafe shekaru suna gwabzawa ba tare da kawo karshensa ba.
Sai dai an samu sabani a sanarwar da suka fitar, inda Vladimir Putin da Volodymyr Zelenskiy suka ayyana lokuta daban-daban game da batun
A kwanakin baya ma dai kasashen sun sanar da tsagaita wuta domin wani bikin addinin Kirista amma sun zargi juna da warware alkawarin da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

