Bamu yarda da hana shan barasa a wuraren shakatawa ba, Masu wuraren shakatawan Abuja

Bamu yarda da hana shan barasa a wuraren shakatawa ba, Masu wuraren shakatawan Abuja

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Bello Mohammed, na shirin fara aiwatar da dokar kulle wuraren shakatawa a birnin daga karfe 7:00 na yamma
  • Masu wuraren shakatawa a birnin tarayyar sun ja hankalin ministan zuwa ga karar da suka shigar gaban babbar kotun FCT kan haka
  • Tun farko an saka wannan doka ne saboda tsaro bayan wasu bata gari sun farmaki wani wajen shakatawa a birnin

Abuja - Gabannin shirinsa na hana siyar da barasa a wuraren shakatawa a Abuja, masu wuraren shakatawa sun rubutawa ministan babbar birnin tarayya, Bello Mohammed wasika don tunatar da shi batun karar da suka shigar a kansa.

Sun yi kira ga ministan da ya riki doka sannan ya saita hadimansa da kuma dakatar da dokar rufe wuraren shakatawa da karfe 7:00 na yamma a babbar birnin tarayyar, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Darakoci 20 ke rige-rigen maye gurbin korarren Akanta Janar

Ministan Abuja
Bamu yarda da hana shan barasa a wuraren shakatawa ba, Masu wuraren shakatawan Abuja Hoto: Leadership
Asali: UGC

A wata wasika da ta fito daga lauyan kungiyar, Ifeanyi Remy Agu, gamayyar ta kalubalanci dokar tilastawa masu wuraren shakatawa rufe kasuwancinsu daga karfe 6:00 na yamma a gaban babbar kotun FCT.

Don haka sun ja hankalin ministan Abujan kan lamarin bayan samun barazana daga babban mai bashi shawara kan sa ido da tabbatar da bin doka, Kwamrad Ikharo Attah, wanda aikinsa ya yi karo da shari’ar da ke gaban kotun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A takardar, Agu ya bayyana cewa ya kamata a ce ana rayuwa cike da yanci inda bin doka ke sama da son rai da cin mutuncin jama'a, Sahara Reporters ta rahoto.

Ya kuma bayyana cewa don an samu lamarin ta’addanci a daya daga cikin wuraren shakatawar ba yana nufin za a samu hakan a sauran wuraren shakatawa ba da zai kai ga sanya dokar tashi karfe 6:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

'Yan fashi sun mamaye lambun shakatawa a Abuja, sun tashi hankalin 'yan hutu

A gefe guda, mun ji a baya cewa wasu ‘yan fashi da makami sun farmaki wani lambun shakatawa na Aco Estate Garden da ke kan hanyar filin jirgin sama a Abuja inda suka yiwa wadanda suka je shakatawa fashin kudade da kayayyakinsu, Daily Trust ta rahoto.

Wani mazaunin yankin, Ezenwa Alfred, ya ce yan fashin wadanda yawansu ya kai shida sun farmaki lambun ne a gefen hedkwatar kungiyar NUT, da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin sannan suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin suka yiwa mutane fashi.

Ya ce yan mintuna bayan nan sai aka fada masa cewa yan fashi da makami sun farmaki lambun sannan sun yiwa wadanda suka je shakatawa fashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel