Mayakan Boko Haram 60,000 sun mika wuya, In ji kwamandan soji

Mayakan Boko Haram 60,000 sun mika wuya, In ji kwamandan soji

  • Mambobin kungiyar Boko Haram sama da 60,000 ne suka mika wuya ga gwamnati cikin shekara daya
  • Kwamandan Operation Hadin Kai da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas, Manjo Janar Christopher Musa, ne ya bayyana hakan
  • Ya bayyana cewa daga cikinsu akwai mazaje 12,000 inda sauran suka kasance mata da kananan yara

Borno - Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas, Manjo Janar Christopher Musa, ya ce yan Boko Haram fiye da 60,000 ne suka mika wuya ga gwamnati a cikin shekara daya da ya gabata.

Janar Musa ya bayyana hakan ne ga jaridar The Sun a karshen makon da ya gabata a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Kwamandan soji
Mayakan Boko Haram 60,000 sun mika wuya, In ji kwamandan soji Hoto: The Sun
Asali: UGC

Ya ce guguwar mika wuya da Boko Haram ke yi daga mabuyarsu a tsakiyar Borno wanda ya fara a watan Yulin 2021, ya yi sanadiyar da mayaka fiye da 60,000 suka hakura da ayyukan ta’addanci.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yan ta’adda fiye da 6,000 sun mika wuya. Wadannan sun hada da masu zuwa filin daga da wadanda basa zuwa. Akwai kimanin mazaje 12,000 a cikinsu, sauran mata ne da yara.”

Ya bukaci yan Najeriya da su yaba da hakan a matsayin hanyar kawo karshen rikicin da ke yankin arewa maso gabas.

Ya ce yadda Boko Haram da ISWAP ke haihuwan yara tare da matansu ko matan da suka sace da yi masu auren dole ya nuna cewa yan ta’addan na gina daular yan ta’adda ne da za su addabi al’umma a gaba.

Ya kara da cewa:

“Abun da suke kokarin yi shine samar da wani karni na yan ta’adda. Idan mace ta haihu, tana daukar sabon ciki bayan watanni hudu. Suna da yara kusan 30,000. Kun ga abun da suke kokarin ginawa.”

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Ya yi bayanin cewa illar samar da kimanin yara 30,000 a cikin jeji da sansanonin Boko Haram, na da girma. Ya ce irin wannan mika wuyar ya ceci kasar daga yan ta’addan gobe wadanda za su girma da sanin cewa yaki ko ta’addanci ba laifi bane.

Ya ce:

“Yana da hatsari saboda idan suka girma a daji, za su yarda cewa ta’addanci ba aibu bane kuma hakan hatsari ne ga kasar.”

Sai dai kuma, ya jadadda cewa dakarun soji za su ci gaba da hurawa sauran yan ta’addan da ke daji wuta.

Ya ce dakarun Operation Hadin Kai za su ci gaba da sawa yan ta’addan zafi haka kuma Operation Lake Sanity na dakarun MNJTF zai mamaye yankunan kan iyaka inda yan ta’addan kan tsere bayan tsananin zafi daga kasar arewa maso gabas.

Rahoton ya kuma kawo cewa kwamandan ya kuma yaba da hange da gudunmawar shugaban hafsan soji Lt Gen Farouk Yahaya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya sake jan-kunnen magoya baya, ya nuna masu hanyar farauto zuciyar mutane

Ya ce fahimtarsa ga yaki da ta’addanci a yankin a matsayinsa na tsohon kwamanda ya taimakawa rundunar wajen samun nasara a kan yan ta’adda.

Burutai: Ba ni da alaka da kayayyakin da ICPC ta kwamushe daga katafaren gidan Abuja

A wani labarin, tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai, ya ce bai da alaka da kayayyakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kwace kwanan nan a Abuja, jaridar The Cable ta rahoto.

Hukumar ICPC a ranar 16 ga watan Yuni ta kai mamaya kan wani gida da ke yankin Wuse 2 a babbar birnin tarayya, kan zargin wawure kudade.

Hukumar ta ce ta kwato kudade da sauran kayayyaki daga gidan ciki harda N175,706,500, $220,965, motocin G-Wagon, BMW kirar 2022 da kuma Mercedes-Benz da kuma wayoyi na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel