Saboda tsaro: Kungiya ta gargadi APC da Tinubu kan tikitin Musulmi da Musulmi

Saboda tsaro: Kungiya ta gargadi APC da Tinubu kan tikitin Musulmi da Musulmi

  • Wata kungiya mai suna ‘Nigeria Democracy Defence Watch’ ta gargadi APC da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, kan tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023
  • Kungiyar ta bayyana cewa gabatar da wannan tikiti na iya haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar nan
  • Ta ce kungiyoyin farar hula musamman na kiristoci za su nuna turjiya a kan wannan yunkurin, kuma za a yiwa Najeriya kallon kasar Musulunci da bangaranci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wata kungiya mai muradin kare damokradiyyar kasar ‘Nigeria Democracy Defence Watch’ ta roki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, da su yi watsi da shirin gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.

Punch ta rahoto cewa kungiyar ta yi wannan rokon ne a cikin wata wasika da ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari mai taken: “Tikitin Musulmi da Musulmi na APC a zaben Najeriya na 2023: Barazana ga kwanciyar hankalin kasa, zaman lafiya da tsaro.”

Kara karanta wannan

Kungiyar Afenifere tayi kira ga jiga-jigan yan siyasan Yarabawa su marawa Tinubu baya

Bola Tinubu
Saboda tsaro: Kungiya ta gargadi APC da Tinubu kan tikitin Musulmi da Musulmi Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

An gabatar da wasikar wacce ke dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Ahmed Adamu da Otunba Adeniji Adegoke, ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli.

A cewar kungiyar, an tura kwafin wasikar ga dukkanin shugabannin cibiyoyin damokradiyya da na tsaro da sauran kungiyoyin kasa da kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce tikitin Musulmi da Musulmi ba wai zai zama barazana ga kwanciyar hankalin kasar bane kawai harma ga zaman lafiya da tsaron kasar.

Kungiyar ta ce gabatar da irin wannan tikitin kamar yadda APC ta bukata zai nuna Najeriya a matsayin kasar Musulunci da bangaranci.

Ta ce miliyoyin mabiya addinin kiristanci a kasar, masu matsakaicin ra’ayi da kungiyoyin fararen hula za su nuna turjiya kan haka.

Ta kara da cewa kungiyoyin al'adu da kabilu da masu wayar da kungiyoyin kasa da kasa su ma za su iya nuna rashin amincewarsu da irin wannan tikitin.

Kara karanta wannan

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

Kungiyar ta ce:

“Don haka muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umurci hukumomin tsaro da su yi abun da ya dace ta hanyar shawartan Bola Tinubu, da jam’iyyar APC kan barazanar da hakan zai iya haifarwa ga tsaron kasar.
“Yana da kyau a kula da abun da yin hakan zai haifarwa ta fuskacin tsaro, musamman idan mutum ya tuna cewa Kiristoci za su tsorata da tikitin Musulmi da Musulmi.
“Suna iya yanke shawarar yin wa’azi da tattara ra’ayoyi a fadin alkaryarsu ta kirista.”

Ta ce kungiyoyin farar hula da dalibai na iya yin zanga-zanga idan aka gabatar da tikitin Musulmi-Musulmi a siyasar a yanayin da ka iya haddasa damuwa ta fuskacin tsaro.

Kungiyar ta yi gargadi kan hadarin da irin wannan tsarin na siyasa zai iya haifarwa ga tsaron nahiyar, jaridar The Guardian ta rahoto.

Magoya bayan PDP a jihar Borno sun fatattaki shugaban jam’iyyar, sun hana shi shiga sakatariyarta

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

A wani labari na daban, fusatattun mambobin PDP a ranar Lahadi, sun mamaye sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri don hana dakataccen shugaban jam’iyyar reshen jihar Borno, Alhaji Zanna Gadama, shiga ofishinsa don gudanar da wani taro da jawabi ga manema labarai.

Gadama ya gayyaci manema labarai don su nadi taron masu ruwa da tsaki da ya kira bayan dakatar da shi da wasu jami’an jam’iyyar suka yi kwanaki da suka wuce, Vanguard ta rahoto.

Sai dai kuma, da shigarsa sakatariyar ya tarar da magoya bayan jam’iyyar wadanda suka mamaye dakin taron inda suka bukaci ya fice daga harabar wajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng