Burutai: Ba ni da alaka da kayayyakin da ICPC ta kwamushe daga katafaren gidan Abuja

Burutai: Ba ni da alaka da kayayyakin da ICPC ta kwamushe daga katafaren gidan Abuja

  • Tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai ya nesanta kansa daga kayayyakin da hukumar ICPC ta kwato daga wani gida a Abuja
  • Buratai ya bayyana lamarin a matsayin kulla-kullan makirai da kuma kokarin da ake yin a bata masa suna
  • Hukumar ICPC a ranar 16 ga watan Yuni ta kai mamaya wani gida da ke yankin Wuse 2 a babbar birnin tarayya, inda ta samo makudan kudade da wasu kayayyaki

Abuja - Tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai, ya ce bai da alaka da kayayyakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kwace kwanan nan a Abuja, jaridar The Cable ta rahoto.

Hukumar ICPC a ranar 16 ga watan Yuni ta kai mamaya kan wani gida da ke yankin Wuse 2 a babbar birnin tarayya, kan zargin wawure kudade.

Kara karanta wannan

Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a wata jiha

Tukur Buratai
Burutai: Ba ni da alaka da kayayyakin da ICPC ta kwamushe daga katafaren gidan Abuja Hoto: PM News
Asali: UGC

Hukumar ta ce ta kwato kudade da sauran kayayyaki daga gidan ciki harda N175,706,500, $220,965, motocin G-Wagon, BMW kirar 2022 da kuma Mercedes-Benz da kuma wayoyi na musamman.

An kuma samo tsadaddun agogunan hannu da dama da kuma takardun wasu kadarori.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko, hukumar ICPC ta ki ambatan sunan mamallakin gidan na Abuja, sannan ana ta ikirarin cewa kayayyakin da aka kwace mallakin tsohon shugaban hafsan sojin ne.

Amma a wata sanarwa kan shafinta na yanar gizo, hukumar ta ce:

“Hujjoji da ke hannu a yanzu sun nuna cewa gidan mallakin mai kamfanin gine-gine na K Salam ne, wani dan kwangilar sojoji.
“Hukumar ta kama manajan darakta na kamfanin gine-gine na K Salam, Mista Kabiru Sallau kuma ana kan gudanar da bincike.”

A halin da ake ciki, da yake martani kan zargin a taron manema labarai a ranar Litinin, Buratai ta hannun mai bashi shawara kan harkokin shari’a, Ugochukwu Osuagwu, ya bayyana rahotannin da ke alakanta shi da gidan a matsayin mai “cike da makirci, mara tushe da kuma hade-hade.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Ya ce:

“Laftanal Janar T.Y. Buratai bai da alaka da wannan gida kuma bai da nasaba da kamfanin gine-gine na said K Salam Construction Company Nigeria Limited. Wadannan karairayi ne da aka tsara don bata sunan Buratai.
“Da farko, ICPC a jawabin manema labarai da ta saki a ranar 24 ga watan Yuni, 2022, ta karyata kasancewar Laftanal Janar T.Y. Buratai da hannu a ciki da binciken da suka yi kan gidan na Wuse 2.
“Abu na biyu, Hukumar Kula da Kamfanoni, a wata wasika mai kwanan wata Litinin, 27 ga watan Yunin 2022 kuma dauke da sa hannun A.G. Abubakar ta fito karara ta nuna babu alaka tsakanin Laftanal Janar T.Y. Buratai da kamfanin K Salam. Mista Muhammed Ahmed Sallau da Sallau Kabiru ne mamallakan wannan kamfani.
“Abu na uku, wani bincike a shafin FRSC na yanar gizo kan lambar mota: ABJ98BH wanda ke makale a motar Mercedes-Benz na karya ne; bincike ya nuna wannan lambar ta wata mota kirar Toyota Corolla ce.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana shirin zaben 2023, tsageru sun kone ofishin INEC na a wata jiha kurmus

“Don haka, muna amfani da wannan damar don umurtan wadanda ke kokarin siyasantar da lamarin da ake kan bincike da su janye.
"Tunda ICPC ta yi Karin haske kan wannan batu, zai zama abin kunya a yi kokarin siyasantar da lamarin."

Osuagwu ya kara da cewar tuni Buratai ya fara daukar mataki kan wadanda suke yada karyar, rahoton Daily Trust.

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

A gefe guda, jam'iyyar PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kira tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya kuma jakaden Najeriya a jamhuriyar Benin, Lt Janar Tukur Buratai.

A wata takardar da kakakin jam'iyyar, Debo Ologunaba ya fitar, jam'iyyar tace a binciki Buratai kan zargin alaka da N1.8 biliyan da ICPC ta samu a wani gida a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

PDP ta bukaci bincikar Buratai kan zargin NSA Janar Monguno, bayan tafiyar janar Buratai na cewa an kwashe dala biliyan daya daga lalitar gwamnati karkashin mulkin APC domin yaki da ta'addanci amma an kasa gano inda suka shiga.

Kara karanta wannan

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

Asali: Legit.ng

Online view pixel