Buhari ya sake nada Hajiya Saratu Umar a matsayin shugabar hukumar NIPC

Buhari ya sake nada Hajiya Saratu Umar a matsayin shugabar hukumar NIPC

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Hajiya Saratu A. Umar a matsayin shugabar hukumar bunkasa jari ta Najeriya
  • Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce an sabonta nadin nata na tsawon shekaru biyar kuma ya fara aiki a nan take
  • Hajiya Saratu ta kawo sauyi a hukumar ta NIPC tsawon lokacin da ta kwashe tana aiki, har ta kai ga samun lambar yabo na musamman

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Hajiya Saratu A. Umar a matsayin shugabar hukumar bunkasa jari ta Najeriya (NIPC) na tsawon wasu shekaru biyar.

An fara nada Hajiya Saratu kan mukamin ne a watan Yulin 2014, jaridar The Nation ta rahoto.

Buhari
Buhari ya sake nada Hajiya Saratu Umar a matsayin shugabar hukumar NIPC Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Malam Garba Shehu, a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 5 ga watan Yuli, ya ce nadin zai fara aiki a nan take.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, sanarwar ta kara da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ta mallaki digiri a fannin tattalin arziki daga jami’ar Ahmadu Bello da kuma digiri na biyu a bangaren lissafin kudi. Ta samu horo a gida da waje a fannin aikinta, da kuma bangaren shugabanci, dabaru, gudanar da harkoki gaba daya da kuma yadda ake tafiyar da harkokin kamfanoni.
“Saratu Umar ta kasance kwararriya a bangaren ilimin fasaha, ta kasance mai kawo sauyi, dabaru, kwarriyua a bangaren tattalin arziki, kwararriya wajen bunkasa jari kuma gogaggiya a bangaren hada-hadar kudi da sauransu.
“A dan lokacin da ta kwashe tana aiki a matsayin babbar sakatariya, ta sauya NIPC zuwa hukumar zuba jari mai daraja a duniya sannan ta rage fitar da kudaden shiga, inda ta adana naira biliyan 500 na kasar, wanda a kansa ta samu lambar yabo daga hukumar tattara kudaden shiga.”

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Hotuna sun nuna lokacin da Tinubu ke matashi, ya halarci jami'a a Turai

Darakoci 20 ke rige-rigen maye gurbin korarren Akanta Janar

A wani labarin, mun ji cewa gwamnati tarayya ta fitar da takardar shirye-shiryen nada sabon akanta janar na tarayya, The Punch ta gano hakan.

A takardar da ta fita ranar 21 ga Yuni, 2022 daga ofishin shugaban ma'aikatan gwamnati na tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, gwamnatin tarayya ta ce:

"Bayan amincewar shugaban kasa, ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ya fara kokarin ganin an nada sabon akanta janar na tarayya daga daraktocin da suka cancanta don zama akanta janar na tarayya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel