'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

  • Yan a mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, suna so a janye batun kulla kawance tsakanin Peter Obi da NNPP
  • Kungiyar goyon bayan Peter Obi tana ganin babu amfanin yin maja a tsakanin obi da Kwankwaso gabannin babban zaben kasar mai zuwa
  • Hakan ya biyo bayan furucin da Kwankwaso ya yi na cewa shi ba zai hakura da kudirinsa na son zama shugaban kasa a 2023 ba

Kungiyar goyon bayan Peter Obi ta nemi a gaggauta kawo karshen duk wasu tattaunawa da ke gudana na yunkurin kulla kawance tsakanin jam’iyyun Labour Party (LP) da New Nigeria Peoples Party (NNPP), jaridar Punch ta rahoto.

Koda dai NNPP ta ce tana tattaunawa da LP kan yiwuwar yin maja, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso ya jadadda cewa ba zai janye daga kudirinsa na neman shugabancin kasar ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP

Peter Obi
'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli, kakakin kungiyar goyon bayan Peter Obi, Onwuasoanya Jones, ya ce bukatar kawo karshen irin wannan tattaunawar ya zama dole tunda Kwankwaso ya ce ba zai janye ba, jaridar The Cable ta rahoto.

Sanarwar ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Don haka ya zama dole a shawarci shugabancin jam’iyyar LP da ya gaggauta janye duk wasu tattaunawa da NNPP, kan batun kulla kawance a tsakaninsu.
“Jam’iyyar NNPP da dan takararta sun sha nuna rashin damuwarsu ga buri da muradin yan Najeriya da suka dade suna shan wahala na samun kasa mai aiki, hadin kai da adalci kuma sun nuna kansu a matsayin wadanda ba za su iya ba kuma basu shirya goyon baya ko shiga tsarin zabar shugaban kasa da zai tabbatar da faruwar hakan ba a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamna a Kaduna ya hada kai da 'yan Shi'a don nemawa Peter Obi kuri'u

“Sakamakon bayyana da ya yi a shirin Politics Today na Channels Tv a kwanan nan, ya goge duk wani kokwanto cewa tunanin dan takarar shugaban kasa na NNPP, Dr. Rabiu Kwankwaso bai yi daidai da na Peter Obi ko jam’iyyar Labour Party ba, musamman kan muhimman batutuwa da suka sa tsohon gwamnan na jihar Anambra neman shugabancin kasar.
“Mai girma Dr. Rabiu Musa Kwankwanso, ya nuna rashin fahimtar halin da Najeriya ke ciki, domin ya tallata kansa ne da farko inda ya fi karkatar da takararsa kan inda ya fito, maimakon inda zai kai Najeriya, ta hanyar bayyana cewa arewa ke ingiza takararsa maimakon yan Najeriya kuma ya fi mayar da hankali kan banbancin kabilarmu maimakon ya dusasar da su.
“Ya kamata mu fahimci cewa tikitin Kwankwaso da Peter Obi zai raba kawunan yan Najeriya masu kishin kasa wadanda suke goyon bayan takarar Peter Obi saboda yarda da suka yi zai kawo hadin kai da yiwa yan Najeriya aiki."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya sun gaji da APC, Kwankwaso ya ce ya hango karshen APC

2023: Tattaunawar haɗa kai tsakanin jam'iyyar LP da NNPP ta rushe, Victor Umeh

A gefe guda, tsohon shugaban jam'iyyar APGA, Victor Umeh, ya bayyana cewa tattaunawar haɗin guiwa tsakanin jam'iyyun LP da NNPP ta ƙare tun ranar 15 ga watan Yuni.

Umeh, wanda ke neman kujerar Sanata karkashin jam'iyyar LP ya ce tattaunawar, "Ta rushe baki ɗaya," saboda kowane ɓangare ya ƙi yarda da wanda zai zama ɗan takarar shugaban kasa.

Tsohon shugaban na APGA ya faɗi haka ne a cikin shirin 'Sunrise Daily' na kafar Talabijin Channels tv ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel