"Aljanna Zai Muku Wahalar Shiga": Martani Kan Wani Wasa Da MC Tagwaye Da Danuwansa Suka YiWa Jinjirarsa

"Aljanna Zai Muku Wahalar Shiga": Martani Kan Wani Wasa Da MC Tagwaye Da Danuwansa Suka YiWa Jinjirarsa

  • Bai barkwanci MC Tagwaye ya bawa mutane dariya a dandalin sada zumunta bayan wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram
  • MC Tagwaye, wanda ke kwaikwayon Shugaba Buhari da dan uwansa sun yi wa yarsa wani wasa da ya daure mata kai
  • An hangi mai barkwancin da dan uwansa a daki daya tare da yarinyar wacce ta kasa banbance wane ne mahaifinta ta rude

Mai barkwanci na Najeriya MC Tagwaye a baya-bayan nan ya nishadantar da mabiyansa a shafukan sada zumunta da wani bidiyo da ya wallafa a instagram.

Tagwaye da dan uwansa da suka yi kama sun hada baki sun yi wa yarinyar wani wasa mai daure kai.

MC Tagwaye
"Aljanna Zai Muku Wahalar Shiga": Martani Kan Wani Wasa Da MC Tagwaye Da Danuwansa Suka Yiwa Jinjirarsa. Hoto: @mctagwaye.
Asali: Instagram

A bidiyon da ya wallafa, Tagwaye da dan uwansa sun shiga dakin da jinjirar ta ke, amma ta kasa gane mahaifinta duba da cewa tagwaye ne su.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

Yar Tagwaye ta dauki lokaci tana kallon mazan biyu cike da rudani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga bidiyon a kasa:

Masu amfani da dandalin sada zumunta sunyi tsokaci

Ieeeraah ta ce:

"Kai wannan ba basu yi adalci ba.... Jinjirar ta rude baki daya.... Za ta rike tunanin wanene mahaifinta."

lady_henriet ta ce:

"Kuma kana tunanin a hakan za ka aljanna."

roselinetasha ta ce:

"Baku kyauta ba gaskiya Duba yadda ta ke kallonsu daya bayan daya. Wato wanene mahaifina a cikinsu? Kunyi sa'a bata fashe da kuka ba."

ejikeasiegbu ta ce:

"Mene yasa kuke rudarta kuna rikatar da ita!"

officialmaryambooth ta ce:

"Mahaifa don Allah ku dena damun ya ta."

aysha_imy ta ce:

"Wannan ba adalci bane har ta kai ga lokacin da ta kame tana tunanin ko dai gane-gane na ke yi Allah ya yi mata albarka❤️."

Kara karanta wannan

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

shoe_culture4us ta ce:

"ku biyu ne ke saka wa jinjirar nan ciwon kai duba paracetamol a gefe."

iggys_feet ya ce:

"Me yasa kuke haka. Ni kaina na rikice balantana wannan karamar gimbiyar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel