Manyan Labarai A Yau
Tun 2019 Lauyoyin EFCC su ka fara binciken Bukola Saraki bisa zargin ya saci kudi daga gwamnati. Shekaru uku kenan har yau ba a yanke hukunci a shari’a ba.
Daruruwan maniyyata aikin hajji a jihar Kano na gudanar da zanga-zanga a Kano kan hana su kujerar hajji duk da cewar sun biya cikakken kudi na hajjin bana.
Sarkin Minna Alhaji Umaru Faruk Bahago, ya shiga lamarin rikici tsakanin kwamishinan yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryad da kwamandan kungiyar yan banga.
Rashin lafiya da matsalar mantuwa ta sa dole Tanko Muhammad ya sauka daga CJN, ya yi ta fama da larura, har abin ya fara bayyana a wajen gudanar da aikinsa.
A safiyar ranar Litinin, 27 ga watan Yuni ne aka wayi gari da labarin murabus din shugaban alkalan Najeriya kuma shugaban majalisar shari’a ta kasa, CJN Tanko.
Kungiyar malaman koyon Larabci da addinin Islama na Najeriya (NATAIS) ta bukaci makarantu a fadin kasar da su mutunta hukuncin kotun koli kan amfani da hijabi.
Duk da yaɗuwar rahoton da ke cewa CJN ya aje muƙaminsa kan rashin lafiya,har yanzun masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari'a sun yi gum da bakin su kan tabbatar da
Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta bayyana cewa shekarun David Ukpo, 'mai bayar da gudummawar koda' wanda ke tsakani a badakalar Ekweremadu 21 ba 15 ba.
Jami’an yan sandan jihar Delta sun kama wani mutum mai shekaru 33, Mista Volt Blessing Gabriel, kan amfani da zarto wajen fille kan dansa mai shekara daya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari