Rabiu Kwankwaso bai cire ran hada-kai da Peter Obi ba, duk da 'Yan hana ruwa gudu

Rabiu Kwankwaso bai cire ran hada-kai da Peter Obi ba, duk da 'Yan hana ruwa gudu

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ce akwai wasu ‘yan hana ruwa gudu a wajen maganar hada-kai da ‘Yan LP
  • Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa yana sa ran Peter Obi ya zama abokin takararsa a zabe mai zuwa
  • Idan dunkulewar NNPP da LP ta gagara, watakila Jam’iyyar ta ba Kingsley Moghalu tikitin mataimaki

Abuja - Har yanzu, Rabiu Musa Kwankwaso yana sa ran cewa akwai yiwuwar a samu fahimtar juna tsakanin New Nigeria Peoples Party da jam'iyyar LP.

A hirar da aka yi da tsohon Gwamnan Kano, kuma ‘dan takarar shugaban kasa a NNPP, ya tabbatar da ana kokarin ganin kansa ya hadu da na Peter Obi.

‘Dan siyasar ya ce har yanzu an gagara samun matsaya ne domin wasu daga gefe su na tsoma baki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Abin da ya sa Peter Obi ba zai iya lashe zaben shugaban kasa a Jam’iyyar LP ba

Kamar yadda Rabiu Kwankwaso ya shaidawa Channels Television a tattaunawarsu ta ranar Lahadi, wasu su na yi wa jam’iyyar LP shiga sharo babu shanu.

Inda gizo yake sakar - Kwankwaso

Inda za a shawo kan lamarin shi ne a samu mutanen da suka cancanta daga bangaren jam’iyyar LP da Peter Obi, ayi magana, la’akari da duba halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta saurari wannan tattaunawa, ta ji Kwankwaso yana cewa babbar matsalar da suke fuskanta a kan hadin-kan, shi ne wanda za a ba tikiti.

Rabiu Kwankwaso
'Dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso a Gombe Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: UGC

Kwankwaso na yi wa Ibo sha'awar su bi NNPP

Shi dai ‘dan takaran na NNPP ya ce yana yi wa mutanen kudu maso gabas kwadayin su samu mulki domin a rika damawa da su, tun da an yi watsi da su.

“Ina da dalilai da suka sa na ke tausayin Kudu maso gabas, ina tunanin cewa hadin-kan NNPP da LP zai rage tashin hankalin da ake ciki a Kudu maso gabas.”

Kara karanta wannan

Abin da ya sa APC ta hana ni damar komawa Majalisa – Sanata ya fayyace komai

“Ba mu son ganin ya zamana wani bangare yana kukan an maida shi saniyar ware. Yanzu haka ana korafi, ana rufe ko ina a garuruwa a duk ranar Litinin.”
“Ana kashe mutane, ana asarar rayuka da damar kasuwanci. Shiyasa na ke amfani da wannan dama domin in ce wannan hadin-kan na mu zai iya yiwuwa.”

Karshe PDP za ta ci riba a bagas

Daily Trust ta rahoto Kwankwaso yana mai cewa muddin shi da Obi ba su dunkule ba, jam’iyyar PDP za ta amfana a yankin na kudu maso gabashin Najeriya.

Idan har ‘dan takaran bai iya shawo kan Obi ya zama mataimakinsa ba, ya ce akwai yiwuwar ya dauko tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu.

Hirar da aka yi da Kwankwaso

Dazu aka ji Rabiu Kwankwaso yana cewa mutanen Kudu maso gabas su na kukan ba a damawa da su, don haka ya kamata NNPP ta ba su damar darewa mulki.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Dattijon Arewa ya soki Atiku da Tinubu, ya yabi Obi da Kwankwaso

Mai neman zama shugaban na Najeriya a karkashin NNPP ya ankarar da Peter Obi cewa babu yadda za ayi mutanen yanki daya su iya ba mutum shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng