Gwamna Ya Ba da Mamaki da Ya Hau Mimbari Ya Yi Hudubar Juma'a
- Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya ya jagoranci huduba da sallar Juma'a a jami'a mallakar jihar a ranar 8 ga wata Mayu 2026
- Tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmad Adamu Mu'azu ne ya gina masallacin kuma shi da kan shi ya halarci sallar Juma'a a jami'ar
- Bayan idar da sallar, gwamna Abdullahi Sule ya zagaya cikin jami'ar jihar Nasarawa, ya gana da mutane daban-daban kafin ya tafi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule ya kara daukar hankalin al'umma bayan ya yi hudubar sallar Juma'a a wani sabon masallaci.
Hudubar ta samu halartar manyan jami'an gwamnatin jihar Nasarawa tare da ministan ilimi, Dr Tunji Alausa da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmad Adamu Mua'zu.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai kan bayanin da gwaman ya yi a lokacin hudubar ne a wani sako da aka wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Disu ya tsoma baki kan zargin kisan Dadiyata
Gwamna Abdullahi Sule ya yi hudubar Juma'a
Gwamnatin jihar Nasarawa ta fitar da sanarwa game da hudubar sallar Juma'a da gwamna Abdullahi Sule ya jagoranta a jami'ar jihar ta NSUK.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnan Jihar Nasarawa, Mai Girma Injiniya Abdullahi A. Sule, ya kaddamar da sabon Masallacin Juma’a na Masjid Halima Al-khair da aka gina a harabar NSUK da ke Pyanku."
"Tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu ne ya gina masallacin tare da sadaukar da shi ga mahaifiyarsa marigayi Hajiya Halima Suleiman Dabo.
"Gwamna Sule ne ya gabatar da hudubar Juma’a tare da jagorantar sallar Juma’a raka’a biyu a masallacin.
"An gudanar da addu’o’i domin zaman lafiya a kasa da kuma neman Allah Ya jikanci Hajiya Halima."

Source: Facebook
Gwamna ya gana da jami'an NSUK
Bayan sallar Juma'a, Gwamna Abdullahi Sule, ya gana da mahukuntan Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, harabar Gudi, shugabannin tsaro da kuma iyayen daliban da aka sace kwanan nan a Gudi.
Rahoton Business Day ya nuna cewa an sace daliban ne daga wajen kwanan su da ke wajen harabar jami’ar NSUK.
Gwamna Sule ya jajanta wa iyalan da kuma al’ummar jami’ar tare da tabbatar musu cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin ceto daliban cikin koshin lafiya.
Wani taro da aka yi a NSUK
Bayan ganawa da iyayen dalibai, Gwamnan Abdullahi A. Sule, ya halarci kaddamar da Mine-Tech Unipod a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi.

Source: Facebook
An bayyana kaddamar da shirin ne a matsayin wani yunkuri na kara inganta bangaren binciken ma’adanai masu daraja.
Daga cikin bakin da suka halarci taron akwai Ministan Ilimi Maruf Tunji Alausa, shugaban TETFUND da kuma wakilan UNDP.
Shettima ya yabi Gwamna Sule
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yaba wa gwamna Abdullahi Sule bisa kawo cigaba a Nasarawa.
Shettima ya bayyana cewa zabo Sanata Ahmed Wadada da Abdullahi Sule ya yi domin ya gaje shi a 2027 abu ne mai matukar kyau.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron tattalin arziki da aka yi a jihar Nasarawa domin lalubo hanyoyi bunkasa arzikin jihar bayan 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
