Abin Kunya: An Kama Matashin da Ya Shiga Gida Satar Ɗan Kamfai na Matar Aure

Abin Kunya: An Kama Matashin da Ya Shiga Gida Satar Ɗan Kamfai na Matar Aure

  • Kotun Majistare a Yola, babban birnin jihar Adamawa ta ba da umarnin tsare wani matashi mai shekaru 27 kan zargin satar ɗan kamfai 22 domin yin tsafi
  • Muktar Shehu ya amsa laifin kutse a cikin gidan matan aure, sata da kuma lalata dukiya a gaban kotu bayan gurfanar da shi
  • Mai gabatar da ƙara daga rundunar yan sanda ya nemi kotu ta ba shi damar gabatar da shaida kafin a ci gaba da shari’ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Adamawa, Nigeria - Kotun Majistare da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai shekaru 27, Muktar Shehu, kan zargin satar kayan dan kamfai na mata guda 22.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin matashin ya saci wadannan wanduna na matan aure ne domin yin asiri, lamarin da ba kasafai ake samun irin wannan ba a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Saurayi ya yi jima'i da budurwa, ya fille mata wuya ta mutu ya sha jinin ta a otel

Kotu.
Gudumar da alkali ke amfani da ita a zaman kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An gurfanar da barawon dan kamfai

Jaridar Leadership ta rahoto cews ana zargin wanda ake ƙarar, mazaunin unguwar Zango da ke Jimeta, ƙaramar hukumar Yola ta Arewa, da aikata laifukan kutse cikin gida, sata da kuma lalata dukiya.

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare ta 3, wadda Uwani Danladi ke jagoranta, bayan jami'an tsaro sun yi nasarar sun kama shi.

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda da mai gabatar da ƙara, Insifekta Danjuma Hamidu, ya gabatar a gaban kotu, ana zargin wanda ake ƙarar da shiga gidan wata mata mai suna Halima Yakubu.

Rahoton da yan sanda suka gabatar

Dan sandan ya bayyana cewa matashin ya kutsa gidan matar aure da ƙarfi a ranar 6 ga Agusta, 2026, tare da satar ɗan kamfanta guda 22 da wasu kayayyakin sawa.

Mai gabatar da ƙarar ya shaida wa kotu cewa yayin da ‘yan sanda ke yi wa Muktar tambayoyi, ya bayyana cewa ya ɗauki kayan ne domin yin tsafi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Bayan karanta masa zarge-zargen da ake yi masa a gaban kotu, Muktar ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su ba tare da ba ta lokaci ba.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Sai dai mai gabatar da ƙara ya nemi kotu ta ba shi damar kiran shaida domin tabbatar da amsar laifin da wanda ake ƙarar ya yi kafin a ci gaba da shari’ar da aka fara.

Daga nan ne kotun ta bayar da umarnin tsare Muktar a gidan gyaran hali da ke Yola, yayin da ake jiran ci gaba da shari’ar, cewar rahoton Daily Post.

An tsare barawon takalma a Kano

A wani labarin, kun ji cewa kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin tsare Muhammad Najib Rimin Kebe a gidan gyaran hali kan zargin satar takalma a masallaci.

‘Yan sanda sun gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dayyabu Jamilu Hamza, inda aka gabatar da tuhume-tuhumen da ake masa.

Rahotanni sun nuna cewa matsalar satar takalma ta dade tana addabar masu zuwa masallacin harabar kotun, musamman a lokutan da ake gudanar da salloli

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262