Gasar Tseren Duniya: China Ta Yi Tsiya, Ta Hana Ƴan Wasan Najeriya Shiga Ƙasarta

Gasar Tseren Duniya: China Ta Yi Tsiya, Ta Hana Ƴan Wasan Najeriya Shiga Ƙasarta

  • Najeriya ta janye daga gasar gudun fanfalaki ta Duniya ta 2025 saboda ofishin jakadancin China ya hana 'yan wasa da jami'an kasar biza
  • Wannan ya wargaza fatan Najeriya na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, duk da kammala shirye-shirye da neman biza da wuri
  • Rashin bizar ya haifar da damuwa game da matsalolin diflomasiyya da kayan aiki da kasashen Afirka ke fuskanta a wasannin duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tawagar Najeriya ta janye daga gasar gudun fanfalaki ta Duniya ta 2025 bayan da ofishin jakadancin China a Abuja ya hana 'yan wasa da jami'an kasar biza.

Wannan lamari, kamar yadda aka bayyana, ya wargaza fatan tawagar Najeriya na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

'Yan wasan Najeriya za su su rasa gasar gudun fanfalaki ta Duniya saboda China ta hana su biza
Tawagar Najeriya: Uko, Ajayi, Oke da Nnamani sun lashe Zinare a gasar gudun fanfalaki ta mita 4x400 a 2021. Hoto: @AfricaStoryLive
Asali: Twitter

Najeriya ba za ta halarci gasar tsere ba

Tawagar Najeriya ta shirya shiga gasa huɗu: Gudun mita 4x100 na maza, 4x100 na mata, 4x100 maza da mata, da 4x400 shi ma maza da mata, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gasar gudun fanfalaki ta Duniya, wacce ke gudana a Nassau, Bahamas, tana da matukar muhimmanci wajen neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta 2025 da za a yi a Tokyo, Japan.

Amma fatan tawagar Najeriya na shiga gasar ya wargaje biyo bayan kin ba da tawagar biza da ofishin jakadancin kasar Sin ya yi domin halartar taron.

China ta hana Najeriya biza duk da bin ka'idoji

A cewar majiyoyi a hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya (AFN), tawagar ta kammala cike dukkanin takardun da ake bukata da shirye-shiryen tafiyar amma kwatsam aka hana su biza duk da sun nema da wuri.

Sai dai ba a ji taka-mai-man dalili na hana bizar ba, amma wannan koma-bayan ya tayar da hankali game da matsalolin diflomasiyya da kasashen Afirka ke fuskanta a wasannin duniya.

Ana ganin wannan ci gaba a matsayin babban koma-baya ne ga ƙungiyoyin gudun fanfalaki na Najeriya, waɗanda suka nuna ƙwarewa a 'yan shekarun nan.

Tun da cancantar shiga gasar Olympics ma tana da alaƙa da yadda aka gudanar da gasar gudun fanfalaki ta Duniya, rashin halartar gasar na iya barin mummunan tabo kan wakilcin Najeriya a fagen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya.

'Yan wasa da jami'an Najeriya sun nuna bacin ransu da Vhina tan hana su bizar zuwa gasar gudun fanfalaki na Duniya na 2025
Tawagar Najeriya: Uko, Ajayi, Oke da Nnamani sun lashe Zinare a gasar gudun fanfalaki ta mita 4x400 a 2021. Hoto: @AfricaStoryLive
Asali: Instagram

Kasashen Afrika na fuskantar matsalolin biza

Jaridar Punch ta rahoto cewa 'yan wasa da jami'ai sun nuna rashin jin daɗinsu game da lamarin, inda wani jami'in AFN wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Abin takaici ne. Waɗannan 'yan wasan sun shafe watanni suna samun horo, kuma wannan babbar dama ce ta tabbatar da matsayinsu a gasar cin kofin duniya.”

Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Duniya ba ta fitar da wata sanarwa game da halin da Najeriya ke ciki ba.

Wannan ba shi ne karon farko da 'yan wasan Najeriya suka fuskanci ƙuntatawa kan tafiya zuwa manyan gasa ba, amma lokaci da muhimmancin wannan gasarya sa ya zama abin takaici sosai.

Tuna baya: El-Rufai ya shiga gasar fanfalaki

A wani labari da muka taba kawo wa, mun ruwaito cewa, Mallam Nasir El-Rufai ya shiga gasar gudun fanfalaki da aka taba shiryawa a 2020 lokacin yana gwamnan Kaduna.

A wancan lokacin, El-Rufai ya shaida cewa an bullo da gasar ne domin zakulo hazikan matasa, da samar da aikin yi da kuma janyo hankalin masu saka hannun jari.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Kaduna a wancan lokaci ta kashe kimanin Naira miliyan 300 wajen shirya gasar, kuma manyan 'yan tseren duniya 10 sun shiga gasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.