'Dan Majalisar Tarayya Ya Zargi Gwamna da 'Hannu' a Ƙaruwar Hare Haren Ƴan Bindiga

'Dan Majalisar Tarayya Ya Zargi Gwamna da 'Hannu' a Ƙaruwar Hare Haren Ƴan Bindiga

  • Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya daga Benuwai, Terseer Ugbor ya ce sakacin da Gwamna Alia ya yi na cikin abin ke kara rura wutar rashin tsaro
  • Hon. Ugbor ya ce gwamnan ya gaza haɗa ka shugabannin siyasa na jihar wajen kawo ƙarshen hare-haren miyagun ƴan bindiga
  • Ya ce duk da yankin da yake wakilata na cikin wuraren da matsalar tsaro ta shafa, ba a taɓa gayyatarsa taron yadda za a tsare al'umma ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Kwande/Ushongo ta jihar Benuwai, Terseer Ugbor, ya dora alhakin karuwar rashin tsaro kan Gwamna Hyacinth Alia.

Hon. Agbor ya ce rashin hadin gwiwa tsakanin shugabannin siyasa na jihar Benuwai, musamman gwamnatin Gwamna Hyacinth Alia ne ka kara dagula sha'anin tsaro.

Hon.Terseer Ugbor
Ugbor ya zargi Gwamna Alia da rashin jawo kowa a jikin domin magance matsalar tsaro a Benuwai Hoto: @TerseerUgbor
Asali: Twitter

Ɗan Majalisar ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV a shirin Sunrise Daily.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi Gwamna Alia ya yi kan batun tsaro?

Ya ce gwamnati mai ci karkashin jagorancin Gwamna Alia ta sa siyasa mara amfani wajen tunkarar matsalar tsaro a jihar Benuwai.

Duk da cewa dukkansu 'yan jam’iyyar APC ne, dan majalisar ya koka da cewa ba a taba gayyatarsa zuwa gidan gwamnati don tattauna matsalolin yankinsa ba.

Ugbor ya ce duk da mazabar da yake wakilta na ɗaya daga cikin mafi fama da matsalar tsaro, gwamna bai taɓa gayyatar zama don tattauna yadda za a tabbatar da tsaro ba.

'Gwamnatin Alia tana siyasa mara amfani'

"Tun da na zama dan majalisar wakilai, ba a taba gayyatata taro gidan gwamnati ba. Na yi kokari na tuntuba, na rubuta wasiƙa, har na kai ga NEMA domin tallafa wa al’umma amma gwamna bai taɓa neman a haɗa kai ba.

- Hon. Terseer Ugbor

Ɗan Majalisar ya bayyana cewa ko da aka kafa kwamitin tsaro daga karamar hukumarsa, ba a gayyace shi ba.

Ya ce hakan ba komai bane illa siyasa mara amfani, “wannan siyasa ce kawai, gurɓatacciyar siyasa. Me kuma zai zama ban da haka?”

Gwamna Alia.
Hon. Agbor ya ce a shirye suke su yi aiki da Gwamna Alia don dawo da tsaro Hoto: Hyacinth Lormem Alia
Asali: Twitter

'Mun shirya aiki tare da gwamna'

Sai dai ya ce su a matsayinsu na wakilai daga jihar, suna da niyyar aiki tare da gwamnan da sauran hukumomi domin kawo zaman lafiya a Benuwai.

Ya ƙara da cewa cewa sama da kashi 40 cikin 100 na filayen noma a jihar Benue sun fada hannun miyagun makiyaya da suka hana jama'a zaman lafiya.

Ugbor ya jaddada cewa rashin tsaro ba abu ba ne da za a sa siyasa ba ko kuma a ware wasu daga cikin 'yan majalisar da ke wakiltar al'umma.

Ya kuma bukaci gwamna da sauran masu ruwa da tsaki su rungumi hadin gwiwa domin ceto jihar daga wannan mawuyacin hali, Daily Post ta ruwaito.

'Yan bindiga sun kashe hakimi a Benue

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe Hakimin Odugbehod a sabon harin da suka kai a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya.

Maharan sun hallaka basaraken ne tare da wani mai suna Jerry John a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025.

Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Marvis Ejeh, ya tabbatar da faruwar lamarin. yana mai cew Cif Adejoh ya rasa ransa ne a gonarsa da ke Akpa-Otobi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262