Bill Gates: Mai Kudin Duniya na 13 Zai Kyautar da Gaba Ɗaya Dukiyarsa, Ya Sanya Lokaci

Bill Gates: Mai Kudin Duniya na 13 Zai Kyautar da Gaba Ɗaya Dukiyarsa, Ya Sanya Lokaci

  • Bill Gates ya sanar da cewa zai ba da kyautar dukiyar sa gaba ɗaya nan da shekara 20, kuma zai rufe gidauniyar BMGF a 2045
  • Mai kudin duniya na 13 a yau ya yanke shawarar sadaukar da dukiyarsa gaba daya domin ceton rayuka da gina al'umma a duniya
  • Bill Gates ya nuna cewa lokaci ya yi da zai kawo karshen ayyukan da ya shafe shekaru yana yi, duk da cewa ya kusanto da lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Bill Gates, wanda ya samar da manhajar Microsoft, ya ce zai ba da dukiyar sa gaba ɗaya a cikin shekaru ashirin masu zuwa.

Bill Gates ya bayyana hakan ne a cikin abin da ya bayyana a matsayin 'babi na ƙarshe na rayuwarsa' a cikin wata kasida da ya wallafa a ranar Alhamis.

Bill Gates ya sanya lokacin da zai kyautar da gaba daya dukiyar da ya mallaka
Mai kudin duniya na 13, Bill Gates. Hoto: Sean Gallup/Getty Images
Asali: Getty Images

Bill Gates zai bayar da kyautar dukiyarsa

A sanarwar da Bill Gates ya wallafa a shafinsa na intanet, wanda Legit Hausa ta gani, attajirin ya ce ya yi tunani mai zurfi kafin yanke wannan babban hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Gidauniyar Bill da Melinda Gates (BMGF) ya kuma sanar da cewa zai rufe wannan babbar gidauniya daga ranar 31 ga Disamba, 2045.

Hamshakin mai kudin da ya shahara da taimakon jama'a, ya ce zai sadaukar da gaba daya dukiyarsa nan da shekaru 20 domin ceton rayuka da gina al'umma a fadin duniya.

Tsohon mafi arziki a duniya, Gates ya jagoranci kirkire-kirkire a fannoni da yawa, ciki har da fasaha, lafiya, noma, makamashi mai tsabta da hanyoyin magance sauyin yanayi, sararin samaniya, ababen more rayuwa, har ma da sufuri.

Darajar dukiyar Bill Gates ta haura $100bn

A halin yanzu, dan shekaru 69 din yana da dukiyar da darajarta ta kai dala biliyan 113.8 kuma shi ne mutum na 13 mafi arziki a duniya, a cewar mujallar Forbes.

Sai dai, Bill Gates ya ƙiyasta darajar dukiyar sa a dala biliyan 108.

"Lokacin da ni da Melinda muka kafa Gidauniyar Gates a shekara ta 2000, mun saka wani sashi a cikin yarjejeniyar farko ta gidauniyar: BMGF za ta daina aiki bayan wasu shekaru da mutuwar mu.
"Shekaru kaɗan da suka gabata, na fara sake tunani game da wannan mataki da muka dauka a wancan lokaci.
"Kwanan nan, na yanke shawarar cewa za mu iya cimma burin gidauniyar a cikin ƙaramin lokaci, musamman idan muka ƙara himma ta hanyar karin kudade a ayyukanmu."

- Bill Gates.

Bill Gates ya ce tun lokacin da ya assafa Gidauniyar Gates shi da Melinda suka kayyade lokacin da za a rufe ta.
Bill Gates tare da tsohuwar matarsa, Melinda Gates. Hoto: @melindagates
Asali: Twitter

Shirin Bill Gates nan da shekaru 20

Ya zuwa yanzu, Gates ya ce gidauniyarsa ta bayar da tallafin sama da dala biliyan 100 - wanda wani bangare ya fito daga hannun Warren Buffett, attajirin duniya na uku.

"A cikin shekaru 20 masu zuwa, za mu ninka adadin gudummawar da muke bayarwa," in ji Gates.

Ya kara da cewa:

"Ina tsammanin gidauniyar za ta kashe sama da dala biliyan 200 tsakanin yanzu da 2045. Wannan adadin ya haɗa da ragowar kuɗin da aka ware da kuma gudummawar da zan bayar a nan gaba.
"Sanarwar ta yau kusan tana nuna farkon babi na ƙarshen rayuwata ta aikin da na shafe shekaru ina yi, kuma na gamsu da wannan matakin da na dauka.
"Yayin da Microsoft ke cika shekaru 50, yana da kyau in yi bikin wannan gagarumin ci gaban ta hanyar bayar da dukkanin dukiyar da na mallaka daga kamfanin."

Bill Gates ya fadi illar dakatar da USAID

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hamshakin mai kudi, Bill Gates, ya ce dakatar da ayyukan hukumar USAID da Elon Musk ya yi ya jawo mutuwar kanana yara a fadin duniya.

Bill Gates ya nuna cewa Elon Musk ya kashe kananan yaran talakawa a duniya, sakamakon rufe USAID ya katse kudaden tallafi da ake aika wa kasashe.

Wanda ya kafa kamfanin Microsoft din ya bayyana cewa dakatar da USAID da Elon Musk ya yi ya sake haifar da yaduwar cututtuka kamar HIV da kyanda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.