Shehu Sani Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Abin da zai Hana Tinubu Zarcewa a 2027

Shehu Sani Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Abin da zai Hana Tinubu Zarcewa a 2027

  • Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
  • Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai iya komawa kan kujerarsa cikin sauƙi
  • Ya nuna cewa dunƙulewa waje guda da ƴan adawa za su yi ne kawai zai iya kawowa shugaban ƙasan cikas a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

ƊEditan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan makomar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2025.

Shehu Sani ya ce Tinubu zai samu gagarumar nasara, idan haɗakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ke jagoranta ba ta tabbata ba.

Shehu Sani, Bola Tinubu
Shehu Sani ya ce Tinubu zai iya lashe zaben 2027 Hoto: @ShehuSani, @DOlusegun
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon Sanatan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani, wanda fitaccen mai rajin kare haƙƙin jama’a ne, ya danganta wannan hasashe da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa.

Me Shehu Sani ya ce kan tazarcen Tinubu

Kwamred ya ce babu wata jam’iyya da za ta iya kayar da Tinubu idan har ya tsaya takara a babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

“Ba za a iya kifar da jam’iyya mai mulki ba sai da haɗakar jam’iyyun siyasa. Haɗaka ce kaɗai za ta sa jam’iyyun adawa su sadaukar da buƙatunsu na ƙashin kansu da muradun siyasa domin amfanin dimokuradiyya gaba ɗaya a ƙasar nan.”
“Za a iya samun haɗaka, amma yadda hakan zai yiwu shi ne abin tambaya. Zuwa yanzu, jam’iyyar SDP ta ce ba ta da sha’awar haɗaka. PDP ta ce ba ta da sha’awa, jam’iyyar LP kuwa kamar tana tafiya ita kaɗai ne, sannan NNPP ma ta ce ba ta da sha’awar haɗaka."

“Kuma idan jam’iyyun adawa suka shiga zaɓe ba tare da ƙawance, haɗaka ko wani irin haɗin gwiwa ba, babu tantama cewa APC za ta yi nasara da rinjaye mai yawa a zaɓen shekarar 2027.”
“Amma idan suka haɗa kai, za su samu kujeru da yawa kuma za su taka gagarumar rawa a siyasar ƙasa."
"Sun sha kaye a zaɓen 2023 saboda rashin haɗin kai, kuma akwai yiwuwar su sake shan kaye idan suka kasa haɗa kai. Idan jam’iyyun adawa suka ƙi haɗuwa da yin ƙawance ko haɗaka, to APC za ta lashe zaɓe."

- Shehu Sani

Shehu Sani
Shehu Sani ya ce sai 'yan adawa sun yi hadaka za su iya kayar da Tinubu Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Shehu Sani ya ƙara da cewa jam’iyyun siyasa a Najeriya ba su da ƙarfi wajen bin wani ra’ayi ko aƙida, wanda hakan ke sanyawa aka maida sauya sheƙa kamar cire riga da sanyawa.

APGA ta amince da tazarcen Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu goyon bayan jam'iyyar APGA kan zaɓen 2027.

Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta APGA ta yarda Tinubu ya zama ɗan takararta a zaɓen.

Soludo ya bayyana cewa jam'iyyun APGA da APC za su yi aiki hannu da hannu domin kawo ci gaba ga al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng