"Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 13,541", Ministan Tsaro, Badaru

"Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 13,541", Ministan Tsaro, Badaru

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana irin tarin nasarorin da dakarun sojoji suka samu a kan ƴan ta'adda
  • Mohammed Badaru ya bayyana cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 13,541 a sassa daban-daban na ƙasar nan
  • Ministan ya nuna cewa an ceto mutane masu yawa da aka sace, yayin da dubunnan ƴan ta'adda suka ajiye makamansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana adadin ƴan ta'addan da dakarun sojojin Najeriya suka kashe.

Ministan ya bada wadannan alkaluma daga watan Mayun 2023 zuwa Fabrairun 2025.

Badaru ya ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda
Mohammed Badaru ya ce sojoji sun ceto mutane daga hannun 'yan ta'adda Hoto: Mohammed Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Ministan tsaron ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Badaru ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 13,541 tare da cafke masu laifi 17,469 a tsakanin wannan lokacin, rahoton Daily Nigerian ya tabbatar.

Sojoji sun samu nasarori kan ƴan ta'adda

Badaru ya ce dakarun sun kuma ceto mutane 9,821 da aka sace, yayin da ƴan Boko Haram da ISWAP guda 124,408 suka miƙa wuya ga sojoji a cikin wannan lokaci.

"Dakarunmu sun dawo da zaman lafiya a ɗaruruwan garuruwa, inda dubban mutane suka koma gidajensu na asali.”
“Misali, daga watan Mayu 2023 zuwa Fabrairu 2025, dakarunmu sun hallaka ƴan ta’adda da masu laifi 13,541. Mun kama 17,469 sannan kuma mun ceto mutane 9,821 da aka yi garkuwa da su."
"A cikin wannan lokaci, ƴan Boko Haram/ISWAP da suka haɗa da mayaƙa da iyalansu guda 124,408 sun miƙa wuya."
"Taƙaitaccen rahoton nasarorin da muka samu sakamakon sabon tsarin haɗin gwiwa ya haɗa da ƙwato makamai 11,118 da harsasai iri-iri guda 252,596."
“Kamar yadda shugaban ƙasa ya tabbatar a jawabinsa na ranar murnar samun ƴancin kai, ya ce an kashe kwamandojin ƴan ta’adda fiye da 300."

- Mohammed Badaru

Badaru ya ce tsaro ya inganta a Najeriya

Badaru ya ƙara da cewa an samu ci gaba matuka wajen inganta tsaro a yankunan da ƴan ta’adda suka lalata a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, inda yawancin ƴan gudun hijira suka koma gidajensu.

Mohammed Badaru
Mohammed Badaru ya ce tsaro ya inganta Hoto: Mohammed Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Ministan ya ce an samu ingantaccen tsaro a titin Kaduna-Abuja da sauran hanyoyi kamar Kaduna-Birnin-Gwari, Funtua-Gusau-Sokoto da Gusau-Kaura-Namoda-Zuru-Jibia.

Ya ce sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun tabbatar da samun ingantaccen tsaro a kasuwanni kamar Niwa, Birnin-Gwari, Kasuandaji da Jibia, inda yanzu kasuwanci ke ci gaba da bunƙasa.

Badaru ya magantu kan makaman ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya yi magana kan batun cewa makaman ƴan ta'adda sun fi na dakarun sojojin Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa ko kaɗan ba haka zancen yake ba, domin sojojin Najeriya sun fi ƴan ta'adda riƙe makamai na zamani.

Badaru ya kuma musanta iƙirarin wasu ƴan majalisa kan cewa ƴan ta'adda sun fara amfani da jirage marasa matuƙa domin kai hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng