Kungiyar AYCF Ta Fadi Manufar 'Yan Siyasar Arewa Masu Sukar Bola Tinubu

Kungiyar AYCF Ta Fadi Manufar 'Yan Siyasar Arewa Masu Sukar Bola Tinubu

  • Ƙungiyar matasan Arewa ta AYCF, ta cacccaki ƴan siyasar yankin masu sukar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban AYCF ya bayyana cewa ƴan siyasar suna yi ne kawai don sun kasa samun muƙami a gwamnatin Tinubu
  • Yerima Shettima ya kuma soki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce bai kamata yana magana da yawun Arewa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar matasan Arewa ta (AYCF) ta yi magana kan wasu ƴan siyasar Arewa da ke sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ƙungiyar AYCF ta yi watsi da su tana mai cewa suna jin haushi ne kawai saboda rashin samun muƙami da kulawa daga gwamnatin Tinubu.

Shugaba Bola Tinubu
Kungiyar AYCF ta soki 'yan siyasan Arewa Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Twitter

Shugaban AYCF, Alhaji Yerima Shettima ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Vanguard a ranar Talata, 6 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me AYCF ta ce kan masu sukar Bola Tinubu?

Ya bayyana masu sukar daga Arewa a matsayin ƴan siyasa masu neman dama waɗanda suka rasa farin jini, kuma yanzu suna dogaro da kafafen sada zumunta don ka da mutane su manta da su.

Alhaji Yerima Shettima ya soki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yana mai zarginsa da cewa rashin samun muƙamin minista a gwamnatin Tinubu ne ya fusatar da shi ya koma sukar gwamnati.

Ya bayyana cewa El-Rufai yana ƙoƙarin magana da yawun Arewa ne don ya ci gaba da zama mai tasiri a siyasar Najeriya.

“Mutane irinsu El-Rufai ya kamata a yi watsi da su, domin ba zai iya magana da yawun Arewa ba. Ya yi gwamna a jihar Kaduna na tsawon shekara takwas, ya kamata ya nuna abin da ya yi wa al’umma."

- Alhaji Yerima Shettima

Ya ƙara da cewa maganganun El-Rufai na kwanan nan suna da nasaba da ɓacin rai na ƙashin kai, ba wai saboda damuwar da yake da ita kan Arewa ba.

“Mutumin nan yana cikin ɓacin rai ne saboda Tinubu bai naɗa shi minista ba. Ya kamata ya manta da hakan ya cigaba da rayuwarsa."
"Ka da ya bayar da kuskuren fahimtar cewa yana wakiltar Arewa ko kuma zai iya yanke mata hukunci a 2027."

- Alhaji Yerima Shettima

Alhaji Yerima Shettima
Yerima Shettima ya bukaci a ba Tinubu lokaci Hoto: Alhaji Yerima Shettima
Asali: UGC

AYCF ta buƙaci a ba Tinubu lokaci

Shugaban AYCF ya jaddada cewa bai dace a riƙa yanke hukunci kan nasarorin Tinubu ba, duba da cewa bai kammala shekara biyu a ofis ba.

Ya roƙi masu sukar gwamnatin Tinubu da su bari ya kammala wa’adin farko kafin su yanke mata hukunci.

“Tun farko mun san wa’adin Tinubu zai kasance mai wahala. Ya gaji ƙalubale da ba za a iya warware su cikin shekara guda ba. Ka da mu tayar da jijiyoyin wuya kawai saboda wasu mutane ba su samu muƙaman da suke so ba."

- Alhaji Yerima Shettima

Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin Abuja a gaban majalisar wakilai.

Shugaban ƙasan wanda ya gabatar da kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 1.78 ya buƙaci majalisar da ta gaggauta amincewa da shi.

Mai girma Bola Tinubu ya nuna cewa amincewa da ƙasafin kuɗin zai taimaka wajen gudanar da ayyukan ci gaba a birnin tarayya Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng