Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya fara tunanin rayuwa idan ya kammala wa'adin mulkinsa. Gwamnan ya bayyana cewa zai koma sana'arsa ta walda.
Indiya ta kai hari Pakistan yayin da Pakistan ta ce ta harbo jiragen yaƙi 5. Indiya ta ce ta kai harin ne kan 'yan ta'adda, ikirarin da Pakistan ta karyata.
Tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Arthur Okowa, ya fito ya kare kansa daga jita-jitar da ke cewa ya mayarwa gwamnatin Delta da Naira biliyan 500.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci wasu daga cikin jihohin Najeriya bayan hawansa mulki. Wasu daga cikin ziyarorin ya yi su ne don kaddamar da ayyuka.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa an samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu dumbin yawa a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa, Auwalu Ɗanladi Sankara ya mauda gwamnati kuɗin da suka ragu a shirin ciyar da marasa galihu da aka yi a Ramadan.
Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta amince da wasu muhimman ayyuka da za su laƙume kudi sama da Naira biliyan 750.
Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan hana shigo da kayayyaki daga waje.
Wata amarya, Saudat ta kashe angonta Salisu a Kano ta hanyar daba masa wuka a wuya bayan aurensu na kwanaki 9. An ce ma'auratan sun yi auren soyayya ne.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari