"Ba saboda Jam'iyya ba ne": Shugaban Majalisa Ya Tsage Gaskiya kan Komawa APC

"Ba saboda Jam'iyya ba ne": Shugaban Majalisa Ya Tsage Gaskiya kan Komawa APC

  • Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
  • Rt. Hon. Blessing Agbebaku ya bayyana cewa ko kaɗan ba tunanin jam'iyya ba ne ya sanya ya fice daga PDP wacce ya lashe zaɓe a cikinta a shekarar 2023
  • Shugaban majalisar ya bayyana cewa komawarsa APC na da nasaba da kare muradun mutanen mazaɓarsa da kuma ganin ya kawo musu ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya bayyana dalilan sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC daga PDP.

Idan ba a manta ba, Blessing Agbebaku tare da wasu ƴan majalisa biyu, Hon. Sunday Fada Eigbiremonlen da Hon. Idaiye Yekini Oisayemoje, sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata.

Blessing Agbebaku ya koma APC
Blessing Agbebaku ya ce saboda kujerarsa ya koma APC Hoto: @Harmless47
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban majalisar ya bayyana dalilin na sa ne yayin da yake sanar da ƴan majalisar sauya sheƙarsa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa shugaban majalisa komawa APC?

Blessing Agbebaku ya ce ya shiga APC ne domin ci gaba da riƙe muƙamin shugaban majalisa, wanda hakan zai amfani mazaɓarsa, rahoton Vanguard ya tabbatar.

"Na koma APC ne domin ci gaba da amfana da muƙamin shugaban majalisa don ci gaban mazaɓata."
“A gare ni, ba jam’iyya nake kallo ba, amma ci gaban yankinmu. Idan na yi watsi da wannan matsayi saboda jam’iyya, wato matsayin da zai kawo ci gaba a yankina, to hakan yana nuna cewa ba ni da niyyar yi wa mutanena hidima."
“‘Yan majalisa masu girma, ina so na sanar da wannan majalisa a hukumance cewa, shugaban wannan majalisa, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC."

- Blessing Agbebaku

Ya samu goyon bayan mutanen mazaɓarsa

Blessing Agbebaku ya bayyana cewa mutanen mazabarsa sun goyi bayan matakin da ya ɗauka na komawa jam'iyyar APC.

Blessing Agbebaku
Blessing Agbebaku ya ce ya koma APC saboda kare kujerarsa Hoto: Rt. Hon. Blessing Agbebaku
Asali: UGC
"Akwai ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a mazaɓar Owan ta Yamma da Gwamna Monday Okpebholo ya fara.”
“Sauya shekar da na yi ba don amfanin kai na bane, sai dai saboda sadaukarwa don jin daɗin mutanen da suka zaɓe ni."
"Siyasa tana da nasaba da muradun jama'a, ba muradina ba, sai dai muradin mutanen da suka ba ni dama na kasance a wannan muƙamin a yau."

- Blessing Agbebaku

Ƴan majalisa sun koma APC daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar dokokin jihar Delta sun sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Ƴan majalisar waɗanda suka haɗa har da shugabanta, sun yi bankwana da jam'iyyar PDP ne wacce aka zaɓe su a ƙarƙashinta, a ranar Talata, 6 ga watan Mayun 2025.

Shugaban majalisar dokokin, Rt. Hon Emomotimi Guwor, ya bayyana cewa sun yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda rikicin da ya da addabe ta a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng