Manyan Labarai A Yau
Wata mata ta yanke al'aurar mijinta a Brazil ta hada miyar wake da ita da wasu sassan jikinsa. Matar ta ce ta aikata haka ne domin ta kama shi yana kallon batsa
'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kai farmaki kan wasu manoma da makiyaya a jihar Borno. 'Yan ta'addan sun hallaka mutane 23 a yayin harin da suka kai.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa babu jam'iyyun siyasa da za a samu a jihar Akwa Ibom a 2027. Ya ce PDP ta tarwatse.
Kotun Ebonyi ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum hudu da suka hada baki suka kashe Chinonso Elom, wani matashi dan Ngbo, a ranar 5 ga Fabrairu, 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa wani abu ya fashe a sashen gas na wani gidan mai a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, mutum biyar sun ji raunuka, motoci sun ƙone.
Wasu daga cikin sanatocin da aka zaba a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP sun sauya sheka zuwa APC. Sun ba da mabambantan ra'ayoyi kan dalilansu na ficeqa daga PDP.
Jam'iyyar SDP ta sanar da naɗa sababbin mataimakan shugaban jam'iyya na ƙasa yayin da batun kawancen ƴan adawa domin kayar da Tinubu ke ƙara kankama.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya yaba da nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan 'yan ta'addan Boko Haram. Ya ba su kyautar kudi.
EFCC ta gurfanar da ɗan China a Legas bisa zargin ta'addanci ta intanet. Kotu ta tura shi kurkuku. A Jos, an ɗaure wasu 'yan China 4 shekaru 5 kan hakar ma'adinai.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari