Wani Abu 'kamar Bam' Ya Fashe a tsakiyar Mutane Ranar Juma'a, An Tafka Asara Mai Yawa

Wani Abu 'kamar Bam' Ya Fashe a tsakiyar Mutane Ranar Juma'a, An Tafka Asara Mai Yawa

  • Wani abu ya tarwatse, wuta ta kama rigi-rigi a sashen gas da ke gidan man Nobpet a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas
  • An ruwaito cewa akalla mutane biyar sun jikkata yayin da motoci da dama suka ƙone sakamakon fashewar yau Juma'a, 16 ga watan Mayu, 2025
  • Jami'an hukumar kashe gobara da dakarun sojin sama sun kai ɗauki a kan lokaci kuma sun yi nasarar kashe wutar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Rahotanni daga jihar Ribas sun tabbatar da cewa wani abu ya fashe a sashen gas na gidan man Nobpet da ke daura da Air Force junction a Fatakwal.

Aƙalla mutane biyar suka ji raunuka sakamakon fashewar wacce ta auku gidan mai yau Juma'a, 16 ga watan Mayu, 2025.

Taswirar Ribas.
Wani abin fashewa kamar bam ya tarwatse a jihar Ribas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ɓarnar da fashewar ta jawo a gidan mai

A rahoton The Nation, shaidu sun bayyana cewa wuta ta kama a wurin kuma ta bazu cikin gaggawa zuwa motoci takwas mallakin wani kamfanin sufuri da ke kusa da gidan man.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa motocin sufurin sun ƙone ƙurmus, kuma mutane sun samu raunin wuta sanadin wannan ibtila'i.

Ɗaukin da hukumar kashe gobara ta jihar Ribas da rundunar sojojin sama suka kai ne ya taimaka wajen shawo kan wutar bayan ta ƙone ababe da dama.

Yadda fashewar ta raunata mutane a Fatakwal

Wani direban motar haya, Emmanuel Ninyaegwu, ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkata, ya ce yana shirin ɗaukar fasinja zuwa jihar Ebonyi tare da matarsa mai ciki lokacin da gobarar ta tashi.

A cewarsa:

“Na bude bayan mota ina shirin loda kaya ne kawai sai na ji ƙarar fashewa, na faɗi kasa, na tashi da gudu na arce, motata ta ƙone.
"Na ji rauni, wasu ma raunukan da suka ji ya fi nawa muni, amma babu wanda ya mutu. An ɗauki wasu zuwa asibiti a motar ujila ta sojojin sama da ta kawo agaji.

"Ƴan kwana-kwana sun zo, amma ruwan su ya ƙare, sai da Sojojin Sama suka kawo taimako, suka kashe wutar gaba ɗaya.”
Yan kwana kwana.
Motoci sun ƙone da wani abu ya fashe a Fatakwal Hoto: Getty Image
Asali: UGC

Ana zargin fashewar ta yi kama da bam

Anthony Ofoke, wani mai motoci biyu da suka ƙone, ya ce abin da ya faru tamkar bom ne ya fashe, kamar yadda Punch ta kawo.

“Na gama lodi na dawo ofis sai kawai na ji fashewa. Ban san abin da zan yi ba sai gudu. Na ji rauni, motoci na biyu sun ƙone, ɗaya bus ɗin haya, ɗaya Sienna.
"Har yanzu jikina yana rawa saboda razana. Jami'an hukumar kashe gobara ne suka taimaka suka ɗaure raunin nan,” in ji shi.

Mista Ofoke ya kuma bukaci gwamnati ta haramta gina gidajen mai a kusa da anguwannin da jama'a ke zaune.

Tanka maƙare da mai ta kama wuta a Neja

A wani labarin, kun ji cewa wata tanka maƙare da man fetur ta kama da wuta a gidan mai na A.A Rano da ke kusa da babban asibitin Kontagora a jihar Neja.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne yayin da ake sauke man fetur daga cikin tankar wajen ƙarfe 7:00 na yamma.

An ruwaito cewa mutane sun shiga fargaba saboda akwai mai a tankunan man da ke ajiye a gidan man lokacin da wutar ta kama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262