Shirin Kayar da Bola Tinubu a 2027 Ya Kankama, SDP Ta Yi Muhimmin Gyara a NWC
- Jam'iyyar SDP ta ƙasa ta naɗa sabbabin mataimakan shugaban jam'iyya daga yankin Arewa da kuma Kudancin Najeriya
- Sakataren SDP na kasa, Araba Rufus Aiyenigba ne ya bayyana sunayen mutum uku da jam'iyyar ta naɗa a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis
- Wannan naɗe-naɗen shugabanni da SDP ta yi na zuwa ne watanni bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya baro APC zuwa jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jam’iyyar SDP ta yi sababbin naɗe-naɗe a kwamitin gudanarwarta na ƙasa (NWC) yayin da batun ƙawancen ƴan adawa ke ƙara kankama a Najeriya.
SDP ta naɗa mataimakan shugaban jam'iyya a shiyyoyin Kudu da Arewacin Najeriya duk a wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Asali: Twitter
Wane gyara SDP ta yi a kwamitin NWC?
Daily Trust ta tattaro cewa SDP ta naɗa Sanata Ugochukwu Uba a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kasa (Kudu) da Farfesa Sadiq Umar Abubakar a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyya (Arewa).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma SDP ta naɗa Mista Hussani Ado Bello a matsayin Sakataren Kudin Jam'iyya na Kasa.
Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda da Sakataren Jam’iyyar SDP na Kasa, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar a ranar Alhamis.
Bayanai kan waɗanda SDP ta naɗa
Sanarwar ta bayyana Sanata Uba a matsayin masani, mai hidima ga al'umma kuma ɗan siyasa daga jihar Anambra, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Ya taba kasancewa Darakta-Janar kuma daga baya ya zama Kwamishina a gwamnatin SDP ta marigayi Gwamna Chukwuemeka Ezeife a Anambra a 1992.
Haka kuma, ya yi aiki a matsayin mamba na cibiyar nazarin dimokuradiyya (CDS) karkashin marigayi Farfesa Omo Omoruyi, a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida.
Sanata Uba ya wakilci mazabar Anambra ta Kudu a majalisar dattawa daga shekarar 2003 zuwa 2007.
A lokacin da yake sanata, ya shugabanci kwamitin harkokin sufuri ta ruwa, kuma ya taka rawar gani wajen amincewa da dokar 'Cabotage'.
Waye mataimakin shugaban SDP na Arewa?
Game da Farfesa Abubakar, sanarwar ta ce shi ƙwararren masani ne a fannin kididdiga, mai digiri na biyu a fannin Huldar Diplomasiyya ta Ƙasa da Ƙasa da kuma digirin digirgir (PhD) a Tattalin Arziki da Ci gaba.
Ya taba zama sakataren jam’iyyar SDP daga 2010 zuwa 2015, sannan ya tsaya takarar gwamna a Gombe karkashin jam’iyyar a 2011.

Asali: Twitter
Har ila yau, ya shugabanci kwamitin shirya babban taron jam’iyyar na ƙasa a shekarar 2011.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"Daga yau waɗanda aka naɗa sun zama mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na jam’iyyarmu mai daraja, SDP, bayan cika duk wasu ƙa'idoji.
SDP ta kara yi wa jam'iyyun PDP da APC illa
A wani labarin, kun ji cewa mambobi sama da 2000 na PDP da APC a jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar SDP.
Ƴan siyasar sun tabbatar da sauya sheka zuwa SDP a hukumance ne a wani babban taron siyasa da aka gudanar a ƙaramar hukumar Dukku.
Taron ya gudana ne tare da bikin buɗe ofishin SDP na ƙaramar hukumar Dukku karkashin jagorancin shugaban jam'iyya na Gombe, Adamu Abubakar Modibbo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng