Ana Fama da Boko Haram, Gwamna Zulum Ya Kafa Sababbin Dokoki a Borno
- Mai girma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kafa sababbin dokoki guda biyu
- Gwamnatin Farfesa Babagana Umara Zulum ya kafa dokar haramta sarar itace ba bisa ƙa'ida ba a faɗin jihar
- Gwamna ya kuma sanar da hukuncin da za a yankewa duk wanda ya karya dokar haramta sare itatuwan ba bisa ƙa'ida ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanya hannu kan wasu dokoki guda biyu.
Gwamna Zulum ya sanya hannu kan dokokin da suka haramta sare itatuwa ba tare da izini ba da kuma wajabta gudanar da aikin tsaftar muhalli na wata-wata a faɗin jihar.

Asali: Original
Jaridar Vanguard ta ce gwamnan ya rattaɓa hannu kan waɗannan dokoki ne a ranar Asabar a fadar gwamnati da ke Maiduguri, a wani ɓangare na yunƙurin daƙile gurɓacewar muhalli da kuma inganta lafiyar jama'a a faɗin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zulum ya sanya doka kan sarar itace
Zulum ya bayyana cewa wannan mataki ya zama wajibi sakamakon yadda ake yanke itatuwa ba tare da tsari ba, wanda hakan ke haifar da matsaloli ga muhalli da kuma barazana ga rayuwar al’ummomi masu zuwa.
Ya kafa hujja da tanade-tanaden da ke cikin sashe na 14(2) da 20 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) a matsayin hujjar dokar da ke ba shi ikon ɗaukar wannan mataki.
Ta hanyar amfani da dokar sare itatuwa, Cap 53, dokokin jihar Borno na 1994, gwamnan ya haramta sare itace daga wannan rana.
Duk wanda aka samu da laifin sare itatuwa zai fuskanci tara ta Naira 250,000 ko zaman gidan yari na tsawon shekaru uku ga laifi na farko.
Wanda ya maimaita laifin kuma, zai fuskanci tara ta Naira 500,000 ko ɗauri na shekaru biyar a gidan gyaran hali.
Za a riƙa tsaftace muhalli a jihar Borno
Doka ta biyu ta ayyana a ranar Asabar ta farko a kowane wata a matsayin ranar tsaftar muhalli, da nufin kara wayar da kan jama'a kan tsafta da hana yaɗuwar cututtuka a cikin al’umma.

Asali: Facebook
Gwamnan ya bayyana cewa duk wanda ya karya wannan umarni zai fuskanci tara ta N100,000 ko zaman gidan yari har na shekaru biyu a karon farko, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Ga wadanda suka maimaita karya dokar tsaftar muhallin, za su iya fuskantar zaman gidan yari har zuwa shekaru biyar.
Gwamna Zulum ya kuma bai wa kotun tsaftar muhalli cikakken iko domin tilasta bin wannan doka a duk faɗin jihar.
An yaba da hana sare itace
Wani mazaunin Biu a.jihar Borno, Aliyu Kabir, ya shaidawa Legit Hausa cewa ya yaba da matakin sanya dokar hana sare itace ba bisa ƙa'ida ba.
"Wannan matakin abin a yaba ne domin sare bishiyoyi ba ƙaramar illa yake yi ga muhalli ba. Muna fatan za a sanya ido sosai don ganin wannan dokar ta yi tasiri."
"Ya kamata a ce duk wanda ya sari bishiya dama zai dasa aƙalla wasu guda biyar."
- Aliyu Kabir
Sojoji sun daƙile harin Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar mafarauta sun samu nasarar daƙile harin ƴan ta'addan Boko Haram.
Jami'an tsaron sun hallaka ƴan ta'addan na Boko Haram guda biyar bayan sun yi yunƙurin kai hari a ƙaramar hukumar Gwoza.
Bayan fatattakar ƴan ta'addan, jami'an tsaron sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa a hannunsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng